AfDB zai tallafa wa Najeriya, Kenya da Zambia da dala milyan 1.3 domin bunkasa noma da kasuwancin mata masu karamin jari

0

Bankin Bunkasa Kasashen Afrika, wato AfDB ya rattaba hannun amincewa da bayar da dala milyan 1.3 domin bunkasa kanan harkokin hada-hadar matan karkara a Afrika.

A cikin kudaden za a bai wa wasu lamuni, wasu kuma inshore, domin bunkasa harkokin su, ta yadda za su shiga cikin sahun wadanda ake damawa da su a hada-hadar kudaden zamani.

Za a raba kudaden a karkashin tsarin ADFIF, tsarin da ke zaburar da mata wajen amfani da tasarifin kudi ta hanyar mu’amala da bankuna.

Matan karkarar da za su amfana da kudaden sun hada da na Najeriya, Kenya da kuma Zambia.

Za a kashe kudaden wajen binciken tsarin yadda matan za su ci moriyar shirin, wanda zai jibinta ne wajen inganta harkokin mata manoma da mata ’yan tireda, ta yadda za su nakalci mu’amala da tsarin tasarifin kudade ta bankuna a zamanance.

“Haka nan wannan tsarin zai kara himma wajen zaburar da matan amfani da fasaha wajen gudanar da harkokin su.” Inji Sheila Okiro, wadda ita ce Babbar Kodinetar Shirin ADFI.

Shirin wanda na tsawon shekaru uku ne, zai amfani akalla mata 360,000, kuma zai kara samar da hanyoyin bunkasa amfanin gona.

Tsarin dai AfDB ya amince da shi a ranar 9 Ga Fabrairu, 2021, zai amfanar da matan da ba su da sukunin iya amfani da harkar hada-hadar kudade ta zamani a yanayin kasuwancin su.

Da zarar fara shirin ya zo, za a kirkiro wata manhajar da matan masu karanan sana’o’i da kuma masu harkar noma za su rika bunkasa harkokin su.

Share.

game da Author