Abubuwa 7 da za su faru da zarar an daina shan taba sigari – Hukumar Lafiya ta Duniya

0

Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana wasu abubuwa har guda 7 da zai faru da mutum da zaran an daina busa taba sigari.

Kamar yadda shafin physiotherapy a Facebook ta zayyano su daki-daki, ba fara dabi’ar busa taba sigari ba abubuwan da za su biyo baya.

1. Bayan mintina 20: Hauhawar jini da saurin bubbugawar zuciya za su ragu.

2. Bayan awanni 12: Gurɓatacciyar iskar nan mai guba (carbon monoxide) za ta daidaita a cikin jini.

3. Bayan sati 2 – 12: Zagayawar jini da aikin huhu za su haɓaka.

4. Bayan wata 1 – 9: Tari da gajercewar numfashi za su ragu.

5. Bayan shekara 1: Haɗarin samun cutar jijiyoyin jini da ke bai wa zuciya jini zai ragu da rabi.

6. Bayan shekara 5: Bayan shekara 5 – 15 da ƙaurace wa shan taba sigari, haɗarin kamuwa da shanyewar ɓarin jiki zai yi daidai da na wanda bai taɓa sha ba.

7. Bayan shekara 10: Afkuwar mutuwa daga cutar dajin / kansar huhu za ta ragu zuwa rabi. Haka nan, haɗarin kamuwa da cutar dajin / kansar baki, maƙogaro, mafitsara, ƙoda da matsarmama za su ragu.

Ƙaurace wa shan taba sigari a yau!

Daga shafin Physiotherapy Hausa

Share.

game da Author