Gwamnan jihar Zamfara ya bayyana cewa akwai wasu da ke yi ya kokarin kawo karshen ƴan bindiga zagon kasa a jihar.
A jawabin da yayi wajen nuna godiya da Hamdala kan sako ɗaliban makarantar Jangebe, Matawalle ya ce ” A daidai muna kokarin tattaunawa da neman sulhu da ƴan bindiga, waɗansu wadanda basu son zaman lafiya suka koma da baya suna danƙarawa ƴan bindigan kuɗi wai kada su sako ɗaliban makarantar.
Matawalle ya ce, tuni har ya sanar da jami’an tsaro su gudanar da bincike akai, kuma shi da kansa ya ce zai bayyana sunan ko su waye.
Daily Trust da ta ruwaito wadannan kalamai na Matawalle ta kara da cewa
gwamnan ya ce sai da suka hada da tattaunawa da neman sulhu kafin suka samu damar ceto ɗaliban daga hannun mahara.
Ceto ɗaliban makarantar Jangebe
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin sako ɗaliban makarantar Jangebe da mahara suka yi ranar Talata.
Gwamnan Matawalle ya tabbatar da dawo da daliban makarantar Jangebe da ‘yan bindiga suka sace a makon jiya.
A hira da gwamna matawalle yayi da Radiyon Tarayya kai tsaye a safiyar Talata, ya ce dalibai 279 ne aka sace ba 317 da ake ta ruwaito wa ba.
” Ba mu biya ko sisi ba wajen karbo daliban makarantar Jangebe ba saboda haka idan ma wasu na ganin wai sai da muka biya wani abu, can ta matse musu. Mu dai ba mu biya ko sisi ba.
” Daliban da aka sace duk mun dawo da su. Wa su daga cikin su na can likitoci na duba su, Ana kuma basu abinci. Za a kai su su huta su yi barci tukunna kafin a mika su ga iyayen su.