A gaggauta yi wa daliban jami’a da ’yan siyasa gwajin tu’ammali da muggan kwayoyi – Buba Marwa

0

Shugaban Hukumar NDLEA na Kasa, Buba Marwa, ya bayyana cewa akwai gaggawar bukatar yi wa daliban manyan makarantun gaba da sakandare da kuma ’yan siyasa gwajin tu’ammali da muggan kwayoyi a kasar nan.

Shugaban na Hukumar Hana Sha da Tu’ammali da Kwayoyi, Buba Marwa, ya ya kuma bayyana cewa kashi 1 bisa kashi 7 na ’yan Najeriya duk su na mu’ammali da kwayoyi daban-daban.

Marwa ya ce bai kamata dalibai da ’yan siyasa masu kan mukami da masu neman mukamai na mulki su kasance wadanda muggan kwayoyi su ka daskare wa kwakwalwa ba.

Marwa ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya kai wa Gwamna Babajide Sanwo-Olu ziyara a Gidan Gwamnatin Jihar Lagos, da ke Marina a ranar Laraba.

Marwa wanda ya jinjina wa Gwamnan Lagos saboda kokarin sa na dakile sha da safarar muggan kwayoyi a Lagos, ya kara da cewa akwai bukatar a rika yi wa dalibai da ’yan siyasa gwajin shan kwayoyi, musamman ma ’yan siyasa masu neman mukamai kafin a kai ga zaben su.

“Shugabanci ko rike babban mukami abu ne na nauyin jama’a a kan mutum. Saboda haka bai kamata a ce an damka jagoranci jama’a ga mutumin da kwakwalwar sa ke daskare da muggan kwayoyi ba.”

Marwa ya kara jaddada wa gwamnan cewa akalla akwai mutum milyan 4.5 masu tu’ammali da kwaya da Jihar Lagos kadai.

“Mun gano cewa cikin mutum bakwai a kasar nan, za ka samu mutum daya na amfani da muggan kwayoyi. Sannan hakan ya kara mana hasken cewa akwai dangantaka tsakanin laifukan da ake aikatawa da kuma san kwayoyi.

“Mu na ganin kamata ya yi a ce Jihar Lagos ce za ta fara yin gwajin tu’ammali da kwayoyi ga dalibai, saboda matasa ne abin ya fi shafa sosai. Musamman wadanda ke manyan makarantun gaba a sakandare da jami’o’i.” Inji Marwa.

Da ya ke jawabi, Gwamna Sanwo-Olu ya ce jihar Lagos na kan aikin gina asibitin warkar da wadanda kwaya ta kwarkwantar da su, har su ka kwarkwance a Ketu-Ejinrin da ke Lagos, domin kokarin dakile illolin da shan kwaya ke haifarwa.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin da Marwa y ace mutum milyan 4.5 a jihar Lagos duk ’yan kwaya ne.

Shugaban Hukumar Hana Sha da Tu’ammali da Kwayoyi ta (NDLEA) Kasa, Buba Marwa, ya bayyana rashin jin dadin yadda ake ci gaba da karin samun yawan masu hada-hada da fataucin miyagun kwayoyi a Jihar Lagos.

Marwa ya bayyana cewa akalla mutum milyan 4.5 na hada-hadar saye, sayarwa, fatauci da safarar muggan kwayoyi a Jihar Lagos.

Ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya kai ziyarar gani-da-ido a ofishin NDLEA na Lagos, inda ya ce dole sai an tashi tsaye an dakile harkar tu’ammali da muggan kwayoyi a Lagos da kasar nan baki daya.

Sannan kuma ya kara da cewa kashi 30 bisa kashi 100 na masu shan muggan kwayoyi a kasar nan, duk a Lagos su ke.

“A kasar nan, an yi kiyasin cewa akalla mutum milyan 15 na hada-hadar muggan kwayoyi a kasar nan. Kuma mutum milyan 4.5 din su duk a Lagos su ke.”

A ziyarar wadda ya kai ta kwanaki uku, Marwa ya umarci zaratan jami’an NDLEA na Lagos su tabbatar sun kakkabe jihar daga muggan ’yan kwaya da sauran masu tu’ammali da ita, kama daga sayarwa, safarar ta da jigilar ta.

Daga cikin dalilan da ya bayar na yawa da tumbatsar hada-hadar kwayoyi a Lagos, har da saboda yawan dimbin jama’ar da ke birnin, tashoshin jiragen ruwa biyu da ke Lagos, filayen jirage da kuma dimbin kantinan sayar da magungunan da ba su da rajista.

Daga nan ya kara da cewa akwai ‘kemis-kemis’ da sauran dakunan sayar da magunguna a cikin kasar nan har guda milyan daya da guda 58,000 a fadin kasar nan.

Ya ce a cikin su, 58,000 ne kadai ke da rajista, amma sauran milyan daya ba su rajista ko ta takardar tsire.

Duk da irin yawan da masu tu’ammali da kwayoyi ke cikin Lagos, hakan bai hana Marwa jinjina wa Kwamandan NDLEA na Jihar Lagos ba, Ralph Igwenagu.

Ya ce ba don kokarin da kwamandan da sauran zaratan jami’an sa ke yi ba, to da tuni masu tu’ammali da muggan kwayoyi a Legas sun wuce yawan da su ke da shi a yanzu.

Share.

game da Author