Shugaban Hukumar NDLEA, Buba Marwa ya bada shawarar a kafa dokar da za ta tabbatar da cewa ba za a bai wa ango aure da amaryar sa ba, har sai ya mallaki shaidar ba shi tu’ammali da muggan kwayoyi tukunna.
Haka kuma ita ma amaryar ta kasance an yi mata gwajin, an tabbatar ba ta tu’ammali da muggan kwayoyi.
“Idan aka shigar da wannan ka’ida a cikin shika-shikan kulla auratayya a kasar nan, na tabbatar da cewa hakan zai iya rage yawan masu shan muggan kwayoyi sosai a kasar nan.”
Marwa ya bada wannan shawara ce a yau Alhamis, wurin wani taro a Ado Ekiti, babban birnin Jihar Ekiti.
Haka kuma a Fadar Gwamnatin Jihar Lagos, a ranar Laraba, sai da Marwa ya bada shawarar a rika yi wa daliban jami’a da ’yan siyasa gwajin tu’ammali da muggan kwayoyi.
Taron dai mai taken, “Hanyoyin Bijire Wa Muggan Kwayoyi”, Ma’aikatar Harkokin Shari’a ta Jihar Ekiti ce ta shirya shi.
Yayin da ya ke nuna damuwa a kan yawaitar tu’ammali da muggan kwayoyi Marwa ya bayyana cewa abin takaice ne matuka a kasar nan a ce Hukumar NDLEA ta kama muggan kwayoyi har na kiyasin naira bilyan 60 a cikin watanni biyun da su ka gabata.
Ya nuna cewa maganar gaskiya irin yawan yadda ake tu’ammali da kwaya da yawan masu shan kwayar a Najeriya abin damuwa ne matuka.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito Marwa a Ekiti ya na cewa, “A yau a Najeriya babu babban kalubalen da ya wuce shan miyagun kwayoyi.
“Misali, ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata ta’addanci ana ganin a wani bangare ne na kasar nan su ka yi kaka-gida. Amma shan miyagun kwayoyi kuwa ya zama hantsi-leka-gidan-kowa a kasar nan baki daya.
“Saboda haka idan aka dakile hanyoyin da masu laifi ke samun muggan kwayoyi, to za a iya rage kashi 50 cikin kashi 100 na muggan laifuka a kasar nan.
PREMIUM TIMES ta buga labarin da Marwa ya bayyana cewa akalla mutum 1 cikin mutum 7 a Najeriya dan kwaya ne.
Haka kuma ya bayyana cewa mutum milyan 4.5 a jihar Lagos, duk ’yan kwaya ne.