TSARO: A bindige ƴan bindiga kawai a wuce wurin, shi ne mafita –Buhari

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya sake jaddada umarnin da ya bai wa jami’an tsaro cewa duk wani da aka gani dauke da bindiga samfurin AK-47, in dai ba jami’in tsaro ba ne, to a bindige shi kawai.

Buhari ya sake jaddada wannan umarni a ranar Alhamis, a lokacin da ya yi taron ganawa da Majalisar Kolin Sarakunan Gargajiya ta Najeriya, wadda Sultan Sa’ad Abubakar III da kuma Ooni na Ife, Adeyeye Ogunwusi su ka jagoranta.

Wannan taro dai a samu halartar Mashawarcin Shugaban Kasa a Harkokin Tsaro, Manjo Janar (ritaya) Babagana Monguno, Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Mohammed Adamu, Babban Daraktan SSS Yusuf Bichi da kuma Babban Daraktan NIA, Ahmed Rufai Abubakar.

Buhari ya jinjina wa jami’an tsaro dangane da nasarorin da ya ce an amu a Arewa maso Gabas da Kudu maso Gabas da wasu yankuna.

“To amma abin da ya fi ba mu mamaki, shi ne abinda ke faruwa a Arewa maso Yamma, inda jama’ar da al’adun su daya, komai daya amma su ke kashe junan su, su saci dabbobin junan su, tare da kone dukiyoyi.

“Dalilin haka ne mu ka yi taro na sa’o’i hudu da shugabannin tsaro mu ka yanke wasu umarni lallai mu ka ce a yi masu daukar gaggawa.

“Wani abu da mu ka tabbatar shi ne, duk wani da aka gani da bindiga samfurin AK-47, to a bindige shi kawai.

“Saboda ita dai AK-47 jami’an tsaro ne kadai aka amince su rike ta.

“Mun rufe kan iyakokin kasar nan. Sai dai kuma rahotannin da na ke samu a kullum na nuna cewa masu garkuwa da mutane da kisan mutane bagatatan a kullum, ba su rasa samun muggan makamai masu tarin yawa.

Buhari ya roki sarakunan gargajiya su yi amfani da matsayin su na iyayen kasa su kara dankon zumunci da hadin kai tsakanin al’umma.

Ya ce hakan zai karfafa kokarin da gwamnati ke yi na ganin an wanzar da daman lafiya a kasar nan.

Sannan kuma ya ja hankalin su su tashi tsaye wajen taimaka wa jami’an tsaro a bankado duk wasu batagarin da ke tayar da zaune tsaye, sun a kashe mutane da garkuwa da mutane a yankunan su.

A wurin taron dai sarakunan daban-daban sun gabatar da bayanan su a madadin al’ummar kowace shiyya, daga cikin shiyyoyin kasar nan hudu.

Wadanda su ka yi jawaban sun hada da Sultan na Sokoto, Ooni na Ife, Obi na Anaca, Etsu Nupe, Jaja na Opbo, Sarkin Bauchi, Sarkin Gwandu da kuma Alawe na Ilawe-Ekiti.

Share.

game da Author