2023: Wallahi Kuyi Hattara, Kashedinku, ‘Yan Uwana, ‘Yan Arewa, Daga Imam Murtadha Gusau

0

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai

Assalamu Alaikum

Ya ku ‘yan uwana ‘yan Najeriya! Ya ku ‘yan uwana ‘yan arewa!! Annabi Muhammad (SAW) yace:

“Duk wanda ya ga abun ki daga cikin ku (wato abun kyama, marar kyawo, wanda zai iya zama hadari ga al’ummah), to yayi kokarin kawar da shi da hannunsa idan zai iya (wato idan shi mai mulki ne, da yake da iko a hannunsa). Idan kuma ba zai iya kawar da shi da hannu ba, to yayi kokarin kawar da shi da bakinsa (ta hanyar magana da baki ko rubutu). Idan kuma duk ba zai iya yin wannan ba, to ya zama wajibi yaki abun a zuciyarsa (wato ya nuna adawa da abun, ya kyamace shi, ya guje shi, kuma kar ya yarda ya goyi bayan wannan abun).” [Bukhari ne ya ruwaitoshi]

Ya ku jama’ah! Da wannan ne nike cewa, hakika, duk mai bibiyar lamurran yau-da-kullun na kasar nan ayau, to zaka tarar yana sane da wasu abubuwa da suke faruwa, musamman a yankin mu mai albarka, wato arewa, da kuma kasar mu mai dimbin daraja, wato Najeriya: kama daga matsalolin rashin tsaro da suka dabaibaye yankin arewa, kamar hare-haren ‘yan ta’addan Boko Haram, zuwa hare-haren ‘yan bindiga dadi, da barayin shanu, da barayin mutane domin neman kudin fansa; da kokarin rusa tsarin tafiyar da ilimin arewa baki daya, ta hanyar satar dalibai maza da mata, da ma malamansu; da rashin samuwar ababen more rayuwa da sauran matsaloli da suka yi wa arewa katutu!

Duk wadannan matsaloli ne da ba wanda ya isa yayi musun samuwar su a arewa, sai munafuki, wanda baya kishin yankin!

A lokacin da muke cikin kuka, da addu’o’i, da kokarin nemo mafita, da kokarin kira ga shugabanni, su nemo hanyoyin magance wadannan matsaloli da suka addabe mu, a lokacin ne kuma wasu lalatattu, gurbatattu, marasa kishi daga yankin arewa, wadanda da ma can su ba arewar ce a gaban su ba, a’a, kawai su me zasu samu, me kuma zasu sa wa aljihunsu, shine kawai a gaban su. Wadannan mutane, ina mai yi maku rantsuwa da Allah, wanda babu abun bautawa da gaskiya sai shi kadai, kuma baya da abokin tarayya, kudi kawai ne a gaban su ba arewa da ‘yan arewa ba.

Daga cikin su akwai wasu ‘yan siyasa daga yankin arewa, akwai wasu gwamnoni daga arewa, akwai wasu sarakuna daga yankin arewa, akwai wasu malaman addini daga yankin arewa, akwai wasu matasa daga yankin arewa, akwai wasu ‘yan kasuwa daga yankin arewa, da dai sauran bangarori na mutane. To sune wai suka hadu, suka sha alwashin sai sun kara kassara arewa, sai sun kara durkusar da arewa, sai sun sayar da ‘yanci da mutuncin arewa, da wasu ‘yan kudi da zasu sa aljihunsu, ko kuma su cika asusun ajiyar su na bankuna.

Wadannan mutane, kamar yadda muke da tabbaci, zasu yi amfani da sarakuna, zasu yi amfani da addini, zasu yi amfani da kungiyoyin addini, zasu yi amfani da malaman addini, zasu yi amfani da wasu matasa, su basu kudi, su saye su, domin su cimma mummunan burin su na cin amanar arewa da ‘yan arewa!

A lokacin da su Dan iska, Sunday Igboho, da shedani Dokubo Asari, da dan ta’adda irin Ganiyu Adams, da shege irin Nnamdi Kanu da sauran ‘yan iska, da ‘yan daba, ire-irensu, da kungiyoyi wadanda aka kafa su domin yakar arewa da ‘yan arewa, irin su Amotekun, suke yiwa arewa da ‘yan arewa barazana akan dukiyoyinsu da rayukansu, ta ko wane bangare, sannan kuma suke kai hare-hare, iri-iri, ga ‘yan uwan mu da ke zaune a yankin kudu, babu wani babba daga cikinsu da ya tsawata masu, bamu ji wani babba daga cikinsu yayi Allah waddai da wannan irin cin mutunci da ake yiwa ‘yan uwan mu ba, wai a lokacin ne wai wadannan shedanu, gurbatattu, ‘yan iska, marasa kishi, wai zasu dauko wani mutum, wai shi Bola Tinubu, suce wai sai sun tursasawa ‘yan arewa sun goyi bayansa, da karfi da yaji! Wadannan mutane su kawai, ba matsalar arewa ce a gaban su ba, ba ‘yan uwansu da ake sacewa, ko ake kashewa kullun ne damuwar su ba, a’a, su damuwarsu ita ce, dole sai sun sayar wa da ‘yan arewa Bola Tinubu! Dole sai sun sa ya samu karbuwa a arewa.

‘Yan arewa mun ce bama son wannan mutum, mun ce bama ra’ayinsa, mun ce baya da wata manufa ta alkhairi gare mu, mun ce su hakura kawai da wannan mutum, mun fada masu gaskiya, amma wadannan mutane sun dage, sun sha alwashi, wai ko muna so, ko bamu so, sai sun kakaba muna Tinubu da karfi da yaji.

Don Allah waye Tinubu? Don Allah wane amfani ne yake da shi ga arewa da ‘yan arewa? Don Allah me ya yiwa Najeriya? Don Allah a lokacin da ake kashe ‘yan uwan mu a yankin su, ana kone masu dukiyoyi, ana yi masu korar-kare, wane irin mataki ne ya dauka, da har wai zaku ce dole sai kun cusa muna Tinubu, da karfi da yaji, duk da kuma mun fada maku ‘yan arewa basu son shi?

Ku ‘yan arewa, muna fada maku, amma kamar kun dauki abun kamar wasa, to yanzu dai gashi nan, ta bayyana a fili karara, cewa abunda muke fada maku gaskiya ne.

Mutanen nan sune suka tsara ziyarar Tinubu zuwa Katsina, wai domin ya kai wa wadanda ibtila’in gobara ya same su a Kasuwar Katsina tallafi na naira miliyan hamsin, wannan wallahi duk siyasa ce, ba domin Allah bane! Shin da can ya kai irin wannan tallafi ga ‘yan uwan mu da suka hadu da jarabawa iri-iri, a arewa? To me yasa sai yanzu? Rainin wayon banza kawai!

Mutanen nan, sune suka shirya wa Tinubu ziyarar Kaduna. Sannan sune kuma suka shirya masa ziyarar Kano. Wai har wani zai shirya wa Tinubu bukin zagayowar ranar haihuwarsa a gidan gwamnatin jiharsa da ke arewa. Wai kuma sun shirya Tinubu zai gana da sarakunan arewa. Kuma fa wannan duk kokari ne na wai dole sai an sayar da Tinubu wurin ‘yan arewa. Don Allah wace irin lalacewa ce wannan? Haba jama’ah, me yasa mu ‘yan arewa kullun muke mayar da kawunanmu shashashu ne? Me yasa ne bama kishin kawunan mu, kamar yadda wadannan mutane ‘yan kudu suke kishin kawunan su, kuma suke kishin yankinsu da ‘yan uwansu?

Koda yake muna da tabbacin cewa, akwai wani gwamna daga arewa, wanda ya dage wai dole shi zai yi tallar Tinubu a arewa, saboda Tinubu yayi masan alkawarin zai ba shi mataimakin shugaban kasa. Sannan kuma yayi masa alkawarin cewa, ba zai bari hukumar EFCC ta bincike shi ba, idan ya zama shugaban kasa. Don haka wannan gwamnan ya mayar da Tinubu Allah sa.

Kuma kar wani munafuki yayi kokarin fassara wannan rubutu nawa da sunan kabilanci. Sam ko kadan, mu ‘yan arewa ba muna kin Tinubu bane saboda kabilarsa ko yarensa, ko yankinsa, ko addininsa, a’a, muna kin sa ne kawai domin rashin dacewarsa, da rashin cacantarsa, da kuma rashin kyakkyawar manufa da yake da ita ga Najeriya baki daya, da kuma yankin mu na arewa da ‘yan arewa!

Don haka mu mutumin kirki muke nema, adili, wanda zai mulkin kasar nan cikin adalci da mutunta ‘yan kasa baki daya, wanda zai yi kokari wurin dawowa da kasar nan martabarta da mutuncinta da ‘yancinta, a samu zaman lafiya da girmama juna, a samu ci gaba da karuwar arziki da tsaro; a kauda yunwa da talauci (da taimakon Allah) tsakanin ‘yan kasa. A kauda kabilanci, da rikice-rikicen kabilanci da na addini tsakanin ‘yan kasa baki daya. A cusa wa ‘yan kasa kishin kasarsu da kaunar zaman lafiya. To mu irin wannan shugaba muke nema, kuma wallahi ko daga wane yanki ya fito, ba ruwan mu. Kuma ko Musulmi ne ko kirista, amma ban da Bola Tinubu, domin shi kam mun san ko waye shi, kuma maitarsa ta fito fili!

Ku sani, kasar mu Najeriya ta dukkanin ‘yan Najeriya ce. Dan kudu ne shi ko dan arewa, Musulmi ne shi ko Kirista, dukkan mu ‘yan kasa ne, ba wanda ya isa ya kori wani daga Najeriya. Sannan kowa yana iya mulkin kasar nan; Dan kudu ne ko dan arewa, Musulmi ne ko Kirista. Amma duk wanda ba mutumin kirki ba, duk mai nuna bangaranci da banbancin kabilanci, baya cikin mutanen da mu ‘yan arewa zamu goya wa baya, kuma ko da dan arewa ne!

Kar ku yarda wasu su rude ku da maganar banbancin kabilanci ko na addini, domin haka Allah ya halicci Najeriya, kuma haka yaso mu zauna da junanmu lafiya. Idan zaku iya tunawa, Annabi (SAW) ya tura Sahabbansa sun zauna karkashin mulkin Shugaba Kirista, adili, wato Najjashi (kafin daga baya ya musulunta). Annabi yace masu:

“Ku tafi garin Sarki Najjashi, ku zauna karkashinsa, wato karkashin mulkinsa, domin shi Kirista ne, kuma shugaba ne adili, yana yiwa kowa adalci, yana ba wa kowa hakkinsa a kasarsa, kuma baya bari a zalunci kowa a kasarsa.”

Kuma Annabi (SAW) ya zauna da Kiristocin Najran lafiya. Yayi sulhu da Yahudawa. Sannan ya shiga cikin yarjejeniyar Hilful Fudul, wadda aka hada kai da Musulmi da wadanda ba Musulmi ba, kai da kowa da kowa, har da mushrikan Makkah, domin a samar da zaman lafiya da tsaro, a samar da ci gaba. A taimaki wanda aka zalunta, sannan a dankwafar da azzalumi ko waye shi. Annabi (SAW) ya shiga cikin wannan yarjejeniya. Kuma daga baya yace, ko yanzu a cikin Musulunci aka nemi in shiga irin wannan yarjejeniya zan shiga, domin amfaninta da kuma alkhairinta.

‘Yan uwana, wannan kadan kenan daga irin tsarin Musulunci da kuma rayuwar Manzon Allah (SAW). Don haka kar wani ya yaudare ku da sunan malanta, ko wani abu mai kama da haka, yace maku haramun ne wanda ba Musulmi ba ya shugabance ku. A kasa irin Najeriya ma ya kamata fadar irin wadannan maganganun ya zama laifi mai zaman kansa, wanda ya kamata a hukunta mutane a kan sa. Domin irin wadannan maganganu na raba kan mutane, wallahi suna daga cikin abubuwan da ke kawo muna tashin hankali da zubar da jinin bayin Allah, da kone dukiyoyinsu a kasar nan. Don haka sai muyi hattara, musamman, da masu ci da addini!

Sannan bamu yarda da yunkurin da wasu gurbatattu, ‘yan cuwa-cuwa suke yi ba, wai na ganin cewa sun tursasawa wasu ‘yan siyasa, su lallashe su, su yaudaresu, wai su jaye, su bar wa Tinubu takara. Sam bamu yarda da wannan tsarin ba, kuma ‘yan arewa ba zasu goyi bayan wannan ba sam!

Sannan mun fada maku, kwangila ce ta musamman, wadannan mutane suka karba daga hannun Tinubu, domin su sa ya samu karbuwa a arewa ko-ta-halin-kaka. Don haka ku sa ido sosai, domin wadannan mutane akwai su cikin bangarori daban-daban. Wani lokaci za’a iya yin amfani da sunan addini. Wani lokaci da wani abun da ba wannan ba.

Sannan ko shakka babu, Tinubu Musulmi ne, to amma ba Musulunci ne kadai ake nema a wurin shugaba ba. Sannan ko Musulmi ko Kirista, duk wanda ya mulki kasar nan ba hukuncin Musulunci zai tsayar maku ba, da kundin tsarin mulki zai yi amfani. Don haka yaudara ne ma kawo maganar Musulunci cikin harkar shugabancin kasa irin Najeriya. Jahilai ake yiwa wannan, idan ana so a yaudare su. Amma ina mai tabbatar maku, duk wanda ke da ilimi, ko na addini ko na zamani, to ba zai yarda da wannan shirmen ba, domin yasan gaskiya!

Daga karshe, ina mai jawo hankalin Sarakunan mu masu mutunci, da malaman mu masu mutunci, da ‘yan siyasar mu masu mutunci, da matasan mu masu mutunci, da kar su yarda da wannan bakar yaudara da ake so a cusa masu, na kokarin tallata masu, da cusa masu mutumin da ko zaman kasar ma a hade bai yarda da shi ba. Shin don Allah ko ba Tinubu bane ya taba cewa shi bai yarda da Najeriya ba? Magana ce a fili wadda yayi, kuma jaridar Punch ta ruwaito, kuma duk ‘yan Najeriya sun ga wannan. To mutumin kuma da ya fadi wannan magana, shine kuma zai dawo yace yana son ya mulki kasar da bai yarda da ita ba, kuma wai har mu saurare shi? Haba jama’ah, me kuke so ku mayar da mu ne don Allah?

Don haka, wallahi ina kira a gare ku da ku kare matsayinku, ku kare girman ku da mutuncin ku. Kar ku goyi bayan Tinubu wurin neman shugabancin kasar nan. Kar ku yarda ayi amfani da ku wurin cin amanar al’ummah. Idan kuwa kun ji ji, to duk abunda ya biyo baya kar kuyi kuka da kowa, kuyi kuka da kawunanku. Sannan ina mai yi maku rantsuwa da Allah cewa, duk wanda ya goyi bayan Tinubu, to sai yayi dana-sanin yin hakan. Kuma idan kunce karya ne, to ku rubuta ku ajiye a kundin tarihinku. Domin wallahi, cin mutuncin da Tinubu zai yi wa arewa da ‘yan arewa idan ya kai ga mulki, ba kadan bane! Kuma ku rubuta wannan ku ajiye. Wata rana idan muna raye, ko mun mutu, zaku ce, ashe abun da bawan Allah nan yake fada muna gaskiya ne!

Sannan ‘yan uwana talakawa ‘yan arewa, ina kira da ku yi karatun-ta-natsu, wallahi kar ku yarda Tinubu ya samu karbuwa a arewa ta-ko-halin-kaka. Ku bar shi ya gama yawace-yawacensa. Ku bar shi ya gama zagaye-zagayensa lami lafiya, amma fa kar wanda ya goyi bayansa.

Kuma muna sane da sojan haya da aka dauka na yara, matasa, zauna-gari-banza, ‘yan zaman-kashe-wando, ‘yan zaman dimama benci, da aka dauka a Kano, domin wai suyi ta ihu, suna hargowa, suna bin motar da Tinubu yake ciki a guje, wai domin a yaudare shi, kuma a yaudari al’ummah cewa, ai ana son sa, ai yana da magoya baya. Wallahi wannan duk karya ce, kuma yaudara ce. Domin wadannan yaran duk biyansu aka yi suyi wannan aikin. Da ma yara ne, matasa, wadanda wadannan mutane suka hana wa ‘yanci, suka hana masu ilimi, suka cusa masu talauci da karfi da yaji, suka mayar da su marasa aikin yi.

Daga karshe, ina rokon Allah ya taimaki Najeriya. Allah ya taimaki arewacin Najeriya, ya hore muna lafiya, da zaman lafiya, da ci gaba mai dorewa, mai amfani. Kuma ina rokon Allah, yasa ‘yan uwana mu gane gaskiya, kuma ya bamu ikon bin ta. Kuma Allah yasa mu gane karya da yaudara, kuma ya bamu ikon guje masu, amin.

Kuma mu sani, ba nayi wannan rubutu bane domin cin mutuncin wani ko kuma farantawa wani rai. A’a, nayi ne domin kishin kasa ta Najeriya mai albarka, da kuma kishin yankina na arewa mai daraja, tare kuma da kokarin bayar da gudumawa wurin samar da shugabanci nagari, wanda kowa zai ji dadi a cikinsa, ba shugabanci irin na ‘yan-jari-hujja ba, irin su Tinubu. Kuma wannan ra’ayin mu ne, sannan bamu hana kowa daukar ra’ayinsa sabanin wannan ba. Amma dai muna da yakinin cewa, gaskiya muke fada maku, kuma tsakaninmu da Allah. Kuma ita gaskiya, daci gare ta, sannan daga-kin-ta-sai-bata.

Sannan don Allah ina roko, idan mutum yana so ya kara sanin ko waye Bola Tinubu, to yayi kokari ya nemi Khudubar Juma’ah, wadda Sheikh Ja’afar Mahmud Adam ya gabatar, a lokacin da kungiyar yarbawa zallah ta OPC tayi wa ‘yan uwan mu ‘yan arewa kisan gilla, a Legas da Shagamu da sauran wurare.

Sannan mutumin nan, ‘yan uwansa, su Sunday Igboho, suna ta cin mutuncin arewa da ‘yan arewa, suna ta kiraye-kiraye akan ballewa daga Najeriya, yaki cewa komai, sannan wasu suce mu goyi bayansa, akan me?

Dan uwan ku, Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuta daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun Imam a lambar waya kamar haka: 08038289761.

Share.

game da Author