2023: Tinubu za mu yi a Arewa Maso Yamma – Shugabannin Majalisun Dokokin jihohin Arewa Maso Yamma.

0

Shugabannin Majalisun Dokokin Jihohin Arewa Maso Yamma ta bayyana cewa da mambobinta da mutanen jihohin Kaf Bola Tinubu za su mara wa baya a zaben shugaban Kasa mai zuwa.

Kakakin majalisar dokokin jihar Legas Mudashiru Obasa ne ya bayyana haka a wata takarda da ya fitar a garin Kaduna ranar Asabar.

Tsohon Kakakin majalisar dokokin jihar Kano Abdullahi Yanshana, ya ce ” Ina tabbatar muku da cewa ba yan majalisa ba kawai, duka mutanen Kano akalla kashi 95 bisa 100 Tinubu za su yi a zaben 2023, wanna ko tantama ba ni da shi akai.

Duk da dai cewa Tinubu bai bayyana niyyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasa ba, shine ke sahun gaba wajen maye gurbin shugaba Muhammadu Buhari idan wa’adin sa ya cika a 2023.

A dalilin goyon baya da gudunmawar da tinubu ya baiwa shugaba Muhammadu Buhari a zabukan da suka gabata tun daga 2015 zuwa zaben 2019, akalar ta fi karkata ga Tinubu cewa shine zai gaji Buhari idan ya sauka.

Idan ba a manta ba Kakakin majalisun dokokin jihohin Kudu Maso Yamma sun bayyana irin wannan goyon baya ga Tinubu a makon jiya.

Har yanzu dai akwai sauran lokaci sai dai kuma hakan bazai hana yan soyasa su fara fitowa suna inda suka dosa idan lokaci yayi.

Gaggan yan siyasan Arewa ne suka halarci wannan taro a Kaduna ranar Asabar.

Share.

game da Author