2023: Tinubu ya fi cancanta zama ‘mujaddadin’ ayyukan Buhari – Mukhtar, Sarkin Matasan Tinubu

0

Wata kungiyar matasan da ke goyon bayan APC ta tsayar da Bola Tinubu ya fito takarar zaben shugaban kasa, ta fara kada masa gangar fitowa takara a zaben 2023.

Wannan kira ya fito ne makonni biyu da wata kungiyar wasu kwararrun matasa su ka tara naira milyan goma domin bayarwa matsayin gudummawar tsayawa takarar zaben 2023, ga Bola Tinubu.

Darakta Janar na Kungiyyar Matasan Sai-Tinubu 2023, Muhktar Muktar, ya bayyana cewa irin ayyukan ci gaban da Tinubu ya dasa a karkashin alfanun dimokradiyya, sun nuna cewa shi jagora ne a kasa baki daya, ba ma a wani bangare na kasar nan kadai ba.

Mukhtar ya yi wannan jawabi a Abuja, lokacin da ya ke hira da manema labarai.

Amma ya smu wakiltar Kodinetan Arewa maso Yamma ne na kungiyar, mai suna Mustapha Abdrahman.

Sai ya yi kira ga Tinubu, wanda ya yi gwamnan Lagos tsaron shekaru takwas da ya yi amfani da gogewa da kwarewar sa da basirar sa, wajen sake wanzar da hadin kai a kasar nan, zaman lafiya da ci gaba.

Ya ce ta hanyar fitowa takarar shugabancin kasar nan a zaben 2023, a karkashin jam’iyyar APC kadai Tinubu zai iya kara wannan dankon hadin kai a fadin kasar nan.

“Tinubu ya shafe sama da shekaru 10 ya na a sahun gaban masu jaddada kasancewar Najeriya zama dunkulalliyar al’umma domin ci gaban al’umma baki daya.

“Tinubu jagora ne, mutum ne mai rainon na kusa da na nesa da shi, ya cicciba su har su kai gaci, mai hada kan al’umma kuma wanda bai san kabilanci a baki ko a aikace ba.” Inji Mukhtar ta bakin Mustapha.

Wannan kira ya fito ne makonni biyu da wata kungiyar wasu kwararrun matasa su ka tara naira milyan goma domin bayarwa matsayin gudummawar tsayawa takarar zaben 2023, ga Bola Tinubu.

Ya ce idan har ya tsaya takarar shugabancin kasa kuma ya yi nasara a karkashin jam’iyyar APC, Tinubu zai zama ‘mujaddadin’Buhari na kwarai, wanda zai dora daga inda Buhari ya tsaya, kuma zai ci gaba da irin kyawawan halayen da Buhari ya dabbaka wajen kawo ci gaba a kasar nan.

Shi ma Sanata Abu Ibrahim wanda ya wakilci Katsina ta Kudu tsakanin 2015 zuwa 2019, ya bayyana irin kyawawan halayen da ya ce Tinubu na da su, wadanda su ka cancanci tsayawar sa takara, duba da irin gagarimar gudummawar da ya bai wa APC har ta samu nasarar kafa gwamnati.

Shugaban Ma’aikatan Sanata Abu Ibrahim, mai suna Mustapha Ahmed ne ya wakilce shi a wurin taron ganawa da manema labarai din.

Share.

game da Author