2023: Har yanzu PDP ba ta damka takarar shugaban kasa a wani yanki ba tukunna –Dattawan Jam’iyya

0

Kwamitin Amintattun Dattawan Jam’iyyar PDP sun bayyana cewa har yau jam’iyyar ba ta damka takarar hugabancin kasar nan a zaben 2023 ga wani yanki ko shiyya ba tukunna, har sai ta warware duk wani cukurkudadden kullin da ke damun jam’iyyar tukunna.

Sakataren Kwamitin Amintattu, Adolphus Wabara ne ya sanar da haka a Abuja, bayan tashi daga taron gaggawa na kwamitin, ranar Laraba da dare, a Abuja.

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Wabara, wanda ya wakilci Shugaban Kwamitin, Walid Jibrin ya ce a yanzu idan aka ce za a yi maganar karba-karba, to an yi hanzari, domin akwai wasu kalubale da ke fuskantar jam’iyyar da ke bukatar a warware su, kafin cimma matsayar karba-karba tukunna.

“Amma idan mu ka warware damuwar da ke tattare da jam’iyya, to daga nan ne kuma za mu fito da batun tsarin karba-karba da za mu tunkari zaben 2023 da shi.

“Amma idan aka ce magana ce kurda-kurdar siyasa, to fa komai na iya faruwa, shi ya sa ma za mu iya gyara kundin tsarin PDP a duk lokacin da mu ka ga dama, domin mu ci zabe.”

Daga nan sai Wabara ya yi kira da ‘yan PDP su rika sara su na duban bakin gatari daga nan har zuwa cikin watan Disamba, lokacin da jam’iyyar za ta yi taron gangamin ta na kasa baki daya.

Ya ce taron gaggawar da Kwamitin Amintattun jam’iyyar su ka gudanar ranar Laraba ya zama wajibi ne ganin irin halin matsalolin da ke addabar kasar nan.

Ya ce taron na so ya tabbatar cewa PDP ta kasance cikin kyakkyawan shiri tsaf, domin kwace goriba a hannun APC, wato kwace mulki a zaben 2023.

Wabara ya jinjina wa Kwamitin Sulhun PDP wanda ke karkashin tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki.

Share.

game da Author