2018-2021: Yadda Aka Yi Garkuwa Da Dalibai Sama Da 800 Cikin Shekara Uku

0

Idan mai karatu bai manta ba an dauke yawan daliban Sakandare na GGSS Chibok, su 276 da Boko Haram su ka yi garkuwa da su daga Jihar Barno a ranar 15 Ga Afrilu, 2014, za a ga cewa sauran garkuwa da satar dalibai da su k auku a bayan wannan, duk a zamanin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari su ka faru.

Yayin da gwamnatin APC ta kafa mulki bisa tunanin ’yan Najeriya cewa za a samu saukin matsalar tsaro, to a bangaren garkuwa da mutane dai matsalar sai ma nunkawa ta yi kusan sau hudu.

Daga ranar 19 Ga Fabrairu, 2018 zuwa 28 Ga Fabrairu, 2021, an kai munanan farmaki a makarantu daban-daban, kuma aka kwashi dalibai masu tarin yawa.

Sai dai kuma dukkan wadanda ake kamawa din, akan sako su daga bisani, amma kuma har yanzu akwai wdanda ke hannun Boko Haram da su ka ki sakin na su.

19 Ga Fabrairu, 2018: Boko Haram sun kutsa cikin sakandaren GSSC ta Dapchi, a tsakar dare su ka yi awon-gaba da dalibai 117.

Ranar 11 Disamba, 2020: Masu Garkuwa sun kamke dalibai har 344 a sakandaren GSC ta garin Kankara, Jihar Katsina.

Ranar 20 Ga Disamba, 2020: Masu garkuwa sun kwashi daliban Islamiyya su 80,a Jihar Katsina, aka yi garkuwa da su.

Ranar 17 Ga Fabrairu, 2021: An yi garkuwa da daliban sakandare su 27 na Kagara, Jihar Neja.

Ranar 26 Ga Fabrairu, 2021: An kutsa cikin makarantar sakandare ta kwana a garin Jangebe, cikin jihar Zamfara, nan ma an waske da dalibai sama da 300.

Kada a manta da wasu dalbai da aka yi garkuwa da su a cikin Jihar Kaduna.

Yawan satar mutane ya fi kamari a makarantun kauye, inda akasari duk a makarantun kauyuka ne ake satar mutane.

Yawancin su kuwa duk ‘ya’yan talakawa ne cikin makarantun gwamnati wadanda ake yin garkuwar da su.

Share.

game da Author