Ƴan bindiga sun kashe shugaban al’umma, jagoran Fulani a Kauru, Jihar Kaduna

0

Jami’an tsaro sun shaida wa gwamnatin jihar Kaduna yadda mahara suka yi wa wani jagoran fulani Lawal Maijama’a, kisan gilla a karamar hukumar Kauru ranar Lahadi.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ne ya bayyana haka ranar Litinin a sako da ya saka a shafinsa ta facebook.

Aruwan ya ce a bayanan da jami’an tsaro suka yi, maharan sun afka wa Alhaji Lawal Musa wanda aka fi sani da Maijama’a a hanyarsa ta dawo wa gida a tsakanin yankin tare da yayan sa.

” Lawal Maijama’a tare da yayan sa Musa Giade suna bisa babur a hanyar su na dawo wa gida sai suka ji harbin bindiga ta ko ina babu kakkautawa.

” Da yake kwana ya kare wa Lawal nan take suka dirka masa harsashi, suka fadi kasa da ga babur din.

” Sai dai shi yayan nasa ya samu ya arce duk da ko an same shi shima da harsashin bindigar.

” Bayan sun cimma Lawal Maijama’a sai suka tsarge wuyar sa har sai da suka ga ba ya numfashi, sannan suka jefar da gangan jikinsa suka kama gabansu.

Aruwan ya kara da cewa gwamnatin Kaduna na jimamin kisan Lawai Maijama’a domin yana daga cikin wadanda ke kokarin matuka na ganin an samu zaman lafiya a wannan yanki.

” Lawal na gaba wajen ganin an samu jituwa tsakanin mazauna yankunan dake karamar hukumar Kauru. Da shi ake tattauna sulhu da kokarin da gwamnati ke yi na ganin an samu zaman lafiya a yanki.

A karshe gwamnan jihar Nasir El-Rufai ya aika ta’aziyyar sa ga iyalan mamacin sannan ya yi addu’ar Allah ya ba dan uwansa lafiya dake asibiti ana duba shi.

Share.

game da Author