A wani rahoton da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna ya fidda ranar Juma’a, mahara sun kashe mutane 13 sannan sun ji wa wasu 7 rauni a hare-hare da suka kai kauyukan jihar Kaduna.
Kwamishina Aruwan ya bayyana cewa wannan bayani na kunshe ne a rahoton jami’an tsaro da ke aikin samar da tsara sassan jihar.
A kauyen Kizachi dake karamar hukumar Kauru kawai mahara sun kashe mutum 10, sunji wa mutum 4 rauni, sannan sun kona gidaje 56 da babura 16, banda kayan mutane da suka jida, suka yi awon gaba da su.
Wadanda aka kashe sun haɗa da
– Esther Bulus
– Maria Bulus jaririya ƴar shekara ɗaya.
– Aliyu Bulus
– Monday Joseph
– Geje Abuba
– Wakili Filibus
– Yakubu Ali.
– Dije Waziri
– Joseph Ibrahim
Sannan an ji wa:
– Cecilia Aku
– Yakubu Idi
– Godiya Saleh
– Moses Adamu rauni da yanzu haka duk suna asibiti ana duba su.
Gwamna Nasir El-Rufai ya mika sakon jajen sa ga iyalan wadanda suka nasu da fatan Allah ya ba wadanda suka ji rauni sauki.