Shugaban gidajen Gyara dabiu, wato Firson dik Kaduna John Mrabure ya sanar cewa sakamakon gwajin cutar Korona da aka yi wa uwargidan Ibrahim El-Zakzaky, Zeenat ya nuna cewa bata dauke da cutar Korona.
Mrabure ya sanar da haka a wani takarda da kakakin hukumar gidajen gyara dabiu Francis Enobore ya raba wa manema labarai ranar Litini.
A watan Janairu PREMIUMTIMES HAUSA ta buga labarin yadda babbar kotu a jihar Kaduna ta bada umurnin a killace uwargidan shugaban kungiyar Shi’a Zeenat bayan bayyana sakamakon gwajin cutar da aka yi mata.
A lokacin alkalin kotun Gideon Kurada ya bada wannan umurni ne bayan lauyan dake kare El-Zakzaky da Uwargidansa, Femi Falana ya gabatar da sakamakon gwajin cutar da ya nuna cewa lallai Zeenat na dauke da cutar.
Falana ya ce a zaman da kotun ta yi ya gabatar da shaidu guda hudu wanda a ciki akwai likitocin da suka yi mata gwajin kuma suka tabbatar ta kamu da cutar.
Ya ce a dalilin haka ne ya roki kotu ta umarci mahukunta su killace Zeenat a wurin dake kula da wadanda suka kamu da cutar, saboda a inda ake tsare da su a Kaduna babu asibiti ko wuri da za a iya duba ta da kyau.