Zan tsaya takarar Shugabancin Jam’iyyar APC idan aka akai kujerar Arewa Maso Gabas – Ali Sherrif

0

Tsohon gwamnan jihar Barno, Ali Modu Sheriff ya bayyana cewa idan har aka kai kujerar shugabancin APC yankin Arewa Maso Gabas, zai yi takarar shugabancin jam’iyyar.

Ali Sherrif ya tsallako daga PDP zuwa APC bayan dambarwar da aka yi wajen shugabancin jam’iyyar PDP da ya kaiga har an yi ta shiga kotu ya daukaka kararraki.

Sherrif ya ce abinda kawai zai iya hana shi takarar shugabancin jam’iyyar APC shine idan ka’idojin da jam’iyyar za ta saka sun haramta mi shi takarar.

” Idan kuka ga ban yi takarar shugabancin APC ba toh, Ka’idojin da jam’iyyar ta saka ne suka taka min birki amma ba dai wani abu ba.

Ali Sherrif ya yaba wa gwamnan Yobe, Mala Buni a lokacin da ya taka mai baya zuwa mazabar sa domin kada kuri’a a zaben kananan hukumomi da jihar ta yi ranar Asabar.

Share.

game da Author