Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya kori manyan darektocin ma’aikatun gwamnatin jihar da masu bashi shawara.
A wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Alhaji Bala Bello ya saka wa hannu ranar Alhamis, Matawalle ya umarci darektocin da aka kora su mika ragamar mulki a hannun ma’ajin ma’aikatun.
Haka suma masu baiwa gwamna shawara, duk an sauke su, kowa ya kama gaban sa, in ji sanarwar Sakataren gwamnati.
Gwamna Matawalle ya ce gwamnati ta yi haka ne domin ta gyara fasali da tsarin aikin gwamnati a jihar.
Bayan haka matawalle ya kirkiro sabbin ma’aikatu har guda uku a jihar.
Ma’aikatun da aka kirkiro sun hada da ma’aikatar al’adun gargajiya, ma’aikatar inganta al’uma da ma’aikatar ilimi.
Zuwa yanzu jihar Zamfara na da ma’aikatu 22.
Discussion about this post