ZAMFARA: Gwamnati ta rufe makarantun kwana dake fadin jihar

0

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya bada umurin a rufe duka makarantun kwana dake fadin jihar.

Hakan ya biyo bayan yin garkuwa da daliban makarantar Sakandaren mata dake Jangebe, Talatan Mafara.

Mahara sun sace dalibai mata har 317 ranar Juma’a.

Gwamna Matawalle ya bayyana cewa tuni gwamnati ta aika da jami’an tsaro domin a ceto wadannan yaran makaranta.

“Za mu rika sanar da iyayen daliban halin da ake ciki.

Matawalle ya yi kira ga mutanen jihar gaba daya da su hada hannu da gwamnati da bata goyon baya don ganin an yi nasaran ceto daliban daga hannu mahara.

“Ina kira ga mutane da kada su yadda a hure musu kunne da shigo da siyasa cikin al’amarin da ya faru domin yin haka ba zai haifar musu da da mai Ido ba.

Idan ba a manta ba a ranan Juma’a ne mahara suka arce da dalibai mata sama a 300 daga makarantar sakandaren mata ta kwana a Jangebe.

Wani dan cikin garin da aka boye sunan sa, ya shaida wa Gidan Radiyon BBC cewa ‘yan bindiga sun kewaye makararantar wajen karfe 1:40 na dare.
Ya ce sun harbi maigadi, amma ya tsere, daga nan sai su ka balle kofar shiga makarantar.

Maharan sun fi su 100. Da su ka shiga, sai su ka fara shiga wani gidan kwanan dalibai, su na cewa “ku tashi lokacin sallah ya yi. Amma su na tashi, sai su ka ga mahara dauke da bindigogi.

Bayan sun tattara su wuri daya, sai da su ka sake bata kusan awa daya da rabi suna harbi a sama. Bayan kamar mintina 20 kuma sai su ci gaba da harbi. Har sai da su ka yi haka kusan awa daya da rabi. Daga nan su ka shiga da yaran cikin daji.

Wanda ake tattaunawar da shi ya kara da cewa an gano wadanda aka tafi da su din sun kai 374, ta hanyar tattara wadanda su ka rage, ana kiran sunaye a rajistar makarantar.

Share.

game da Author