ZABEN 2023: Tinubu nagartacce ne, gangariyar da ba sai an sha wahalar tallata shi ba – Inji Tsohon Minista

0

Tsohon Ministan Ayyuka, Dayo Adeyeye ya bayyana cewa jigon jam’iyyar APC Bola Tinubu ne ya fi cancanta jam’iyyar APC ta tsayar takarar Shugaban Kasa a zaben 2023.

Adeyeye wanda shi ne Shugaban Ajandar Maida Mulki Kudu Maso Yamma a 2023, ya bayyana haka a ranar Lahadi, a lokacin da ‘yan kungiyar su ka kai ziyara ga basaraken nan Akarigbo na Remoland, Babatunde Ajayi a Jihar Ogun.

“Shi fa Tinubu nagartaccen dan takarar ne, wanda ba a bukatar shan wahalar tallata shi. Mutum ne da ya bayar da gudummawa wajen kawo ci gaba a kasar nan baki daya.”

“Mu na da shiyyoyi uku a kudancin kasar nan, kuma kowace shiyya ta na son shugaban kasa na 2023 ya fito daga bangaren ta. Amma ina da tabbacin cewa Bola Tinubu ne kadai zai iya ciwo mana tikitin zaben 2023.

“Ya gina ‘yan Najeriya da dama a ko’ina cikin kasar nan. Babu ruwan sa da kabilanci ko addinanci. Ya hada yankunan kasar nan sun dinke a karkashin inuwar siyasa daya.

“Don haka mun tattaru ne domin yi masu kamfen. Idan har za mu iya kimtsa gidan mu, to za mu samu nasarar maido da kujerar shugaban kasa a shiyyar Kudu maso Yamma.”

Duk da dai har yanzu Tinubu bai fito fili ya nuna sha’awa ko aniyar tsayawa takara ba, tuni wannan kungiya ta Ajandar 2023 ta fara yi masa kamfen gadan-gadan.

Cikin makon da ya gabata ma shugabannin kungiyar sun kai irin wannan ziyara a Jihar Oyo.

Share.

game da Author