ZABEN 2023: A damka wa dan kudu mulki kawai a wuce wurin – Kabiru Gaya

0

Tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Kabiru Gaya, ya ce idan dai har ana so a yi adalci da cika alkawarin sharuddan zamantakewa, to idan zaben 2023 ya zo, bar wa dan kudu takara, kuma a zabi dan kudu kawai, a wuce wurin.

Ya ce babu wata ja-in-ja, dan kudu ne ya cancanci ya gaji Shugaba Muhammadu Buhari.

Gaya wanda shi ne Shugaban Kwamitin Zabe na Majalisar Dattawa, ya yi wannan ikirari a taron ganawa da manema labarai, wanda NAN ta shirya, ranar Talata a Abuja.

Ya ce tunda dai har Arewa ta yi zango biyu a jere, to babu wani tawilin da za a kawo a ce wai dan arewa ne zai kara yin shugabanci a zaben 2023.

“ Dukkan yankunan biyu kowane ya gamsu da zamantakewa tare, don haka zaben 2023, kawai a zabi dan kudu ya gaji Shugaba Buhari a wuce wurin.

“ Na yi amanna cewa yanzu ya dace shugaba ya fito daga kudu, amma mataimakin sa ya fito daga Arewa.

“ Ya kamata Najeriya ta zama kasa daya dunkulalliya, a ci gaba da kaunar juna cikin zamantakewar lumana. A bar wa dan kudu shugabanci a zaben 2023. Dan Arewa sai ya kasance mataimakin shugaban kasa.”

Maganar Kabiru Gaya ta zo daidai lokacin da ake ta hankoron cewa a bar wa dan kudu mulki ya shugabanci kasar nan, bayan Buhari ya kammala shekarun sa takwas. Musamman, akwai masu ganin cewa a kudu din ma kamata ya yi a bar wa kabilar Igbo su shugabanci kasar nan, domin ba su tai yin zababben shugaban kasa ba, tun bayan dawowar jamhuriya ta uku, daga 1999 zuwa yau.

Sai dai kuma yayin da wasu jigajigan APC irin su Kabiru Gaya ke cewa akwai yarjejeniyar fahimta tsakanin kudu da Arewa a batun mulkin karba-karba, wasu kuma na cewa babu wata yarjejeniya a rubuce, kawai a zabi cancanta ba dan kudu ko dan Arewa ba.

Ko a cikin jam’iyyar PDP akwai wannan sabani, abin ya ja Gwamna David Umahi na Ebonyi komawa APC daga PDP, saboda ya yi zargin cewa PDP ta shirya ba za ta bai wa dan kudu takarar shugaban kasa a zaben 2023 ba.

Ko cikin makon da ya gabata, an yi wata hira da tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, inda ya ce ya rantse da Allah Buhari ba zai ba Bola Tinubu takarar shugaban kasa a 2023 ba.

Share.

game da Author