Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru, ya baiwa yan kudu mazauna jihar tabbacin kare rayukansu da dukiyoyin su.
Gwamnan ya bayar da wannan tabbacin ne a ranar Asabar yayin ziyarar da Gwamnan Jihar Ebonyi, David Umahi, ya kai Jihar ta Jigawa.
Gwamna Badaru ya gayyaci gwamnan Ebonyi don ƙaddamar da aikin hanyoyi na cikin gari da yayi a ƙaramar hukumar Babura da ke jihar.
Sannan kuma ya yi amfani da wannan dama wajen yin jawabi ga ‘yan kudu mazauna jihar Jigawa wadanda suka halarci taron don yi wa Umahi maraba da zuwa jihar.
“Muna farin ciki cewa ƴan kudu dake zaune a Jigawa suna zaune lafiya tare da mu, kuma muna so ku isar da sakon zaman lafiya a duk fadin kasar cewa mutanenku suna cikin aminci da kwanciyar hankali a Jigawa da kuma arewa.
“Ka gaya wa wadancan masu yin zagon kasa, ƴan siyasar da ke son haifar da rikici a kasar nan cewa ba za su yi nasara ba saboda ba za a dauki fansa a arewa ba. Domin kuwa yin hakan shine kulle-kullen su na kawo ruɗani da tada hankalin jama’a don kasa ta wargaje.
Gwamnan ya ce gwamnati zata tsare duk wani ɗan kudi dake zaune a Jigawa ba za ta bari a muzguna masa ba. “Wannan shi ne sakon da muke so ka isar da shi gida idan ka koma jihar ka domin muma a nan hakan ne matsayar mu.
A nashi jawabin gwamnan jihar Ebonyi, Umahi, ya jinjina wa gwamnonin Arewa da ke ta kokarin kwantar da kawunan mutanen yankin kada a samu barkewar tashin hankali ko tarzoma.
” Muna godewa mutanen arewa musamman matasa saboda yadda suka yi jajirce da a zauna lafiya da kuma hadin kan Najeriya a matsayin tsintsiya madaurinki ɗaya, ina mai tabbatar maku da cewa, mu gwamnonin Kudu maso gabas da shugabanninmu, muna kan tare da wannan manufa ta ku do kuma yin tir da duk wani barazana don raba kasar nan da wancakalar da hadin kan kasar nan.
“A duk fadin Najeriya akwai mutanen kirki da marasa marasa kirki, wata nagari da baragurbi, ba kamata a riga danganta ayyukan ta’addanci da batagari da kabila ko addini ba. Za mu ci gaba da samarwa kowa da kowa tsaro a jihohin mu.