Babban Hafsan Tsaron Kasa, Manjo Janar Lucky Irabor, ya ce a karkashin jagorancin sa Gwamnatin Tarayya za ta kula da dukkan hakkokin da su ka wajaba da wadanda su ka kamata a bai wa sojojin da ke bakin dagar yaki da Boko Haram a kasar nan.
Irabor ya ce hakan ma zai kara masu kwarin guiwar kara maida hankali sosai tare da sa himmar ganin an dakile Boko Haram nan ba da dadewa ba.
Ya yi wannan bayanin a ranar Lahadi a Maiduguri, a lokacin da ya ke wa dakarun Najeriya jawabi a Babbar Cibiyar .
Irabor ya samu rakiyar Babban Hafsan Askarawan Najeriya, Manjo Janar Ibrahim Attahiru, wanda ya canji Tukur Buratai, Shugaban Hafsoshin Jiragen Ruwa da na Sama.
Ya ce ita kan ta cibiyar za a kara inganta ta.
“Shugaba Muhammadu Buhari ya ce mu isar da gaisuwar sa gare ku, kuma ya na kara yi maku jinjina, kamar yadda ya ke yi maku a kullum.
“Mun gana da shi, inda ya ce mu sanar da ku cewa kara kulawa da jin dadin ku shi ne abu mai muhimmanci a gaban sa da gaban gwamnatin sa baki daya.
“Ni da sauran Shugabannin Tsaro baki dayan mu mun jaddada kudirin ganin cewa duk wani abu da mu ka tabbatar idan mun yi zai kara inganta kulawa da ku da kuma aikin ku, to za mu yi shi.
“A gaishe ku da aikin fama mazajen fama, zaratan yaki. Ku ci gaba da kishi da maida himma. Ba mu da wani zabi sai mu ga cewa mun sauke dukkan nauyin da Babban Kwamandan Askarawan Najeriya ya dora mana.
“Ina fatan ba za ku gaji da ganin mu ba, domin za mu rika kawo ziyara nan akai-akai. Wannan zai kara tabbatar maku cewa a koda yaushe mu na tare da ku domin ganin wannan fafatawa da ku ke yi ta zo karshe nan ba da dadewa ba a cikin nasara.”