Yunkurin kirkiro rigakafin cutar korona a Najeriya tatsuniya ce – Farfesan Cututtuka

0

Cikin wata tattaunawa da aka yi da shahararren masanin cututtukan nan Farfesa Daniel Oluwayelu, ya bayyana cewa bai ga ta yadda za a yi har a iya kirkiro rigakafin cutar korona a Najeriya ba.

Waka Daga Bakin Mai Ita: “Ni dai a iyakar sani na da ilmin da na ke da shi, batun za a iya kirkiro allurar rigakafin cututtukan dan Adam a Najeriya, kwata-kwata ba abu ne ba mai yiwuwa ba a Najeriya.

“Rabon da a ce an kirkiro wata rigakafin allura a Najeriya tun cikin wadda aka kirkiro a Cibiyar Kwajin Rigakafi ta Gwamnatin Tarayya cikin 1991…”

Farfesan ya ce fitar da naira bilyan 10 domin fara kokarin kirkiro allurar rigakafi a Najeriya, wani yunkuri ne mai kyau a wani bangaren.

“Sai dai kuma magana ta gaskiya abu ne da ba ma zai taba yiwuwa a kirkiro rigakafin a Najeriya ba, saboda ba mu da cibiyar bincike da gwajin rigakafin a Najeriya.

“Cibiyar da mu ke da ita ta tarayya da ke Yaba, Legas, rabon da ta yi aiki shekaru da dadewa. Ta ma zama kamar makwancin fatalwa, komai ya lalace. Ta na bukatar makudan kudaden da za a farfado da ita.

“Sannan cibiyar na bukatar kwararrun ma’aikatan da aka tabbatar sun kware, kuma su san abin da su ke yi wajen iya sarrafa kayan gwaji da binciken cututtuka na fasahar zamani da ake amfani da su a yanzu, ba irin na shekarun baya ba.

“Ka ga ashe maganar a ware naira bilyan 10 a ce a kirkiro rigakafin korona a Najeriya, wannan zance ne kawai. Akwai sauran batutuwan da ba a maida hankali a kan su ba. Sai aka maida hankali wajen fitar da kudin kawai.”

Ya kara da cewa abinda kawai Najeriya ta rika tabukawa shi ne samar da rigakafin cututtukan dabbobi a Cibiyar Binciken Cututtukan Dabbobi ta Vom, da ke Jihar Filato.

Farfesan ya ce ya san cibiyar ta rika kirkiro rigakafin dabbobi har ta na sayarwa a cikin kasar nan da sauran kasashen Afrika.

Ya ce an rika sayar da rigakafin cututtukan shanu, awaki har da na kaji da sauran su.

“Amma abin haushin shi ne, sai dai kuma magana ta gaskiya abu ne da ba ma zai taba yiwuwa a kirkiro rigakafin a Najeriya ba, saboda ba mu da cibiyar bincike da gwajin rigakafin a Najeriya.

“Cibiyar da mu ke da ita ta tarayya da ke Yaba, Legas, rabon da ta yi aiki shekaru da dadewa. Ta ma zama kamar makwancin fatalwa, komai ya lalace. Ta na bukatar makudan kudaden da za a farfado da ita.

“Ministan Harkokin Lafiya da ya sauka kafin wanda ke kai a yanzu, ya yi kokarin farfado da cibiyar gwajin rigakafin gwamnatin tarayya, tsawon shekaru uku ya na kokari. Amma shi ma hakar sa ba ta cimma ruwa ba.’’

Sai dai kuma ya kara da cewa akwai wasu daidaikun masana da ken a su kokari a bayan fage, daga wani tallafi da su ke samu ba daga gwamnati ba, To amma su din ma abin ba zai iya kai gaci ba, saboda rashin wadatattun kudade.

Share.

game da Author