Yaya gaskiyar batun cewa wai ruwan nonon mata na iya kashe kwayar cutar COVID-19? – Binciken Dubawa

0

Zargi: A wani bincike da cibiyar Dubawa ta gudanar don gano sahihancin labaran da aka rika yada wa a shafukan sada zumunta a yanar gizo, twitter da facebook cewa wai ruwan nono na iya kashe kwayar cutar da ke janyo COVID-19, ko labaran kanzon kurege ne kawai, ga abinda ta gano.

Yaduwar Korona – (Covid-19)

Yaduwar Korona (coronavirus) a kasashen duniya na cigaba da janyo fargaba musamman yadda ta shafi mata masu shayarwa, domin ana zaton cewa jarirai na iya kamuwa da cutar daga ruwan nono idan har uwa na dauke da ita.

A yanzu haka dai, akwai binciken da ke cewa akwai nau’in SARs-CoV-2 wanda ke haddasa cutar ta COVID-19 a ruwan nonon mai shayarwa, akwai kuma wanda ke cewa babu.

Ba da dadewa ba, wani mai amfani da shafin sada zumunta ta Facebook, mai suna Sadiq Alabi ya sanya hoton wani labari dangane da shayarwar. Alabi ya dauko labarin ne daga twitter, a shafin wata mai suna Karleen Gribble (@DrKarleen G) ranar laraba goma ga watan Fabrairu 2021.

A cewar Dr Karleen Gribble, ruwan nonon iyaye matan da ke dauke da COVID-19 ba shi da SARs-CoV-2 sai dai nau’in da ke rigakafin cutar.

“Ba’a sami nau’in SARs-CoV-2 a ruwan nonon matan da ke dauke da COVID-19 ba, an dai sami antibodies SARs-CoV-2. Kuma bayan da aka sanya SARs-CoV-2 a cikin ruwan nonon, sai nonon ya kashe ta.”

Tantance gaskiyar wannan magana

Dubawa ta bi diddigin shafin twitter da ya kasance asalin wannan batu, inda a takaitaccen bayanin da Dr Karleen Gribble ta bayar game da kanta ta ce ita farfesa ce a jami’ar Western Sydney da ke Australiya, inda ta ke da kwarewa a fannonin shayar da jarirai, kula da yaran da suka raunata da kuma kula da marayu.

Dubawa ta samu wannan bayani a shafinta inda mutane 1,023 ke bin ta, kuma a ranar alhamis 11 ga watan Fabrairu, 2021 ta sanya labarin a shafinta.

Daga nan, Dubawa ta bi diddigin rahoton da ta bayar a matsayin hujjar da ke goyon bayan batun, inda ta gani cewa bincike ne da wata cibiya mai suna Bio ta gudanar kuma wata Kungiyar masu bincike mai zurfi kan illimin halitta ko kuma American Society for Microbiology ta wallafa.

Rahoton mai suna “Yanayin Kwayoyin Halitar SARs-CoV-2, Garkuwar Jiki da Yiwuwar Narkewarsa a Ruwan Nonon Mata masu Dauke da cutar COVID-19” ya nuna cewa kwayoyin halittan SARs-CoV-2 a ruwan nonon matan da ke fama da kadan zuwa matsakaicin COVD-19 na da sinadaran da ke kashe SARs-CoV-2, wadanda kuma ke inganta garkuwar ruwan nonon.

Daga nan Dubawa ta cigaba da bincikenta a rahotanni da takardu daban-dabn da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta wallafa dangane da COVID-19 da shayarwa. Hukumar Lafiya ta Duniyar ta ce daga binciken da aka gudanar zuwa yanzu, babu alamun nau’in SARs-CoV-2 a ruwan nono.

Kadan daga cikin rahoton binciken WHO dangane da shayarwa…..

Rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) kan Shayarwa da COVID-19

Ruwan nono ne abinci mafi inganci wa jarirai har da wadanda aka tabbatar cewa iyayensu na dauke da cutar coronavirus. Muddin mace mai shayarwar tana daukan matakan da aka gindaya daga kasan wannan binciken, tana iya shayar da jinjirinta ba tare da wata matsala ba. Ruwan nono na da sinadaran da ke kare garkuwar jikin jarirai ya kuma taimaka wajen karesu daga kamuwa da cututtukan da suka shafi numfashi. Akwai hujjojin da ke jaddada mahimmancin shayarwa da ma rawar da ya ke takawa wajen girma da bunkasar kananan yara, da kiwon lafiyarsu da kuma yadda zai taimaka wajen kawar da wasu cututtukan da ka iya zuwa nan gaba.

Mene ne hadarin shayar da Jariran?

Har yau babu nau’in kwayar cutar da ke janyo COVID-19 a ruwan nono. Sai dai duk da haka, cutar sabuwa ce kuma binciken da ke goyon bayan wannan hujar kalilan ne. Jami’an kiwon lafiya na cigaba da gano hanyoyin da kwayar cutar ke yaduwa da ma irin hadarin da ya ke da shi ga jarirai da mata masu shayarwa.

Kuna iya kallon wani hoton bidiyon da Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi kan shayarwa tare da hadin kan kawancen kungiyoyin kula da lafiyar mata da jarirai da kuma ta lafiyar kanana yara wato PMNC idan kun latsa nan.

Haka nan kuma, Hukumar da ke Yaki da Bazuwar Cututtuka (CDC) ta goyi bayan cewa mata masu shayarwar da ke dauke da COVID-19 su wanke hannayensu da sabulu da ruwa kafin su dauki jariransu, sannan su sanya kyalen rufe baki da hanci a yayin da suke akalla kafa shida daga jariran (Har sadda suke shayarwa ko daga mama ko daga kwalba)

Daga Karshe

Batun cewa ruwan nono na kashe nau’in SARs-CoV-2 wato kwayar cutar da ke janyo COVID – 19 gaskiya ne. Kungiyoin WHO da CDC duk sun ba da tabbacin cewa ruwan nono ba zai iya zama mafarin kamuwa da cutar ba.

Ko da ya ke, wajibi ne a yi la’akari da rahoton Hukumar Lafiya ta Duniyar da ya nuna cewa COVID-19 sabuwar cuta ce, kuma binciken da ke nan yanzu babu yawa. Wannan na nufin cewa nan gaba sakamakon binciken na iya sauyawa. Sai dai jam’an lafiya na cigaba da yin gwaji dan gano yadda cutar ke yaduwa da kuma hadarin da ke tattare da shi musamman wajen mata masu shayarwa da jariransu.

Share.

game da Author