Yari ya sake fadawa tarkon EFCC kan wasu biliyoyin naira da ya nemi canja musu wuri a wani bankin Najeriya

0

Tsohon gwamnan jihar Zamfara AbdulAziz Yari, ya sake fadawa tarkon hukumar EFCC in da ya bayyana a ofishin hukumar dake Legas domin amsa tambayoyin kokarin canja wa wasu biliyoyin naira wuri dake dankare a wani bankin kasar nan.

Hulumar ta tsare Yari na wani lokaci mai tsawon gaske a Legas yana yi mata bayani akan wannan kudade biliyan 300 da yake kokarin canja musu wurin zama daga wani bankin Najeriya.

Sai dai majiya ta shaida mana, bayan Yari ya kammala amsa tambayoyi daga jami’an hukumar EFCC sun umarce shi ya tafi, amma kuma idan ana bukatar wasu bayanan zai ga sammaci.

Wannan tuhuma ya zo kwanaki kadan bayan gwamnati ta kwace wasu kudaden tsohon gwamnan, wanda suka tabbata na shi ne amma kuma ya kasa bayyana gaban kotu yayi mata bayanin bayanin yadda ya same su.

Kudaden da ke jibge a wasu asusun bankuna daban daban na kwance ya kasa gagagra bayyana a kotu domin ya fadi yadda ya same su. Ganin haka kotu ta ce tunda mai kudin ya nuna rashin gaskiya akai ya ki bayyana ya bada hujjojin mallakar kudade ta yanke hukuncin a kwashe su kaf a maida asusun gwamnati.

An kwace masa dalar Amurka 56,056.75 a asusun Polaris Bank, sai kuma naira milyan 12.9 da kuma wasu naira milyan 11.2.

Akwai kuma wasu zunzurutun dalolin Amurka ajiye har dala 301,319.99 wadanda su ma kotu ta kwace.

Sannan an kwace naira 217,388.04, sai kuma wasu dala 311,872.15 da ya boye a Zenith Bank, wadanda su ma kotun ta kwace daga hannun sa.

Babbar Mai Shari’a Ijeoma Ojukwu, ta ce kotu ta kwace kudaden kamar yadda EFCC ta roki kotun ta yi, tunda Yari ya kasa bada kwakkwaran bayanin yadda ya tara kudaden, a matsayin sa wanda ba dan kasuwa ba.

Share.

game da Author