Wasu Yarabawa mazauna kasashen waje sun kirkiro Gidauniyar Tallafin Korar Fulani Makiyaya.
Gidauniyar mai suna GoFundMe, sun kafa ta ne domin tallafa wa gogarman fatattakar Fulani makiyaya daga jihohin Yarabawa.
An kafa gidauniyar domin a tara kudaden sayen motoci da sauran ‘kayan aikin duk da ake bukata’, wadanda za su samar da tsaro a jihohin, a fafutikar da Sunday Igboho ke yi.
PREMIUM TIMES ta gano cewa Yarabawa mazauna ketare sun yanke wannan shawara ce a wani zama da kungiyar ta yi a ranar Talata.
Taron dai ta intanet aka yi, wato kowa ya halarta daga gida ko ofis, wato ‘virtual’.
Babban wanda ya fara taimakawa da kudi dai shi ne Maureen Badejo, wani mai kafar sadarwa wato ‘blogger’ kuma dan taratsi da ke zaune Birtaniya. Shi ne ya bude gidauniya da alkawarin bayar da gudummawar fam 100,000.
Wadannan kudade su na kwatankwacin naira milyan 51.8.
Ya zuwa ranar Alhamis da safe har an tara naira milyan 4.8, wato fam 9,320.
Igboho ya bayar da wa’adin korar Fulani a yankin Ibarapa, jihar Oyo. Bayan kwana bakwai ya ja zugar ‘yan daba aka auka masu da kone-kone, har aka kone gidan Sarkin Fulani, kuma aka tilasta shi yin gudun hijira zuwa jihar Kwara.
Tuni Igboho ya dira jihar Ogun inda rahotanni su ka tabbatar an banka wa wasu rugagen Fulani makiyaya wuta.
Sai dai kuma wasu shugabannin Yarabawa, ciki har da 0oni na Ife, Etinan Ogunwusi, ya gargadi Igboho ya yi a hankali, ya bar hukuma ta yi aikin ta.