Rundunar ‘Yan Sandan Babban Birnin Tarayya Abuja, ta karyata wani rahoto da ya bayyana cewa sun gano wata masana’antar da aka ceto mata 115 masu shayarwa, wadanda ake tatsar nonuwan su ana sarrafa madarar sayarwa.
Kakakin ‘Yan Sandan Abuja, Mariam Yusuf, ta yi cikakken bayani a ranar Talata a Abuja, inda ta warware zare da abawar cewa zancen ji-ta-ji-ta ce, karairayi ne da kuma soki-burutsu.
Wani rubutu ne aka rika watsawa a soshiyal midiya, wanda aka yi ikirarin cewa ‘yan sanda sun kamo ko kuma sun ceto wasu mata 115 masu shayarwa ko masu jego, wadanda ake tatsar nonuwan su ana hada madarar sayarwa a wani gida, ko karamar masana’anta a Abuja.
“ Rundunar ‘Yan Sandan Babban Birnin Tarayya (FCT) na sanarwa da babbar murya cewa wannan labarin ba gaskiya ba ne, karya ce, domin ba mu gano wani gida da ake tatsar ruwan nonuwa maijego ana hada madara ba.
“Saboda haka rundunar na kara nesanta kan ta da wannan karairayi, kuma ta na bada shawarar cewa jama’a su sanar da ita idan ma akwai irin wurin da hakan ke aruwa ko ya taba aruwa, idan har gaskiya ne.” Inji Mariam.
Ta kuma bada lambobin da jama’a za su rika kira idan har bukatar jami’an tsaro da gaggawa ta kama, dangane da wasu laifukan da wasu batagari ke aikatawa: 08032003913, 08061581938, 07057337653 and 08028940883.
Discussion about this post