Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta kama wani magidanci mai suna David Idibie da ya kashe matarsa da duka.
Kakakin rundunar ƴan sanda Olumuyiwa Adejobi ya sanar da haka ranar Laraba yana mai cewa Idibie ya kashe matarsa mai suna Juliana Idibiea lokacin da ya rika dukan ta babu kakkautawa bayan sun samu sabani a gidan su.
Adejobi ya ce jami’an tsaron sun iske gawar Juliana a gidan ma’auratan dake layin Joado, Oke Ira Nla, Ajah bayan wani makwabcinsu ya kawo kara ofishin ‘yan sanda.
“A daren Talata Juliana da mijinta Idibie sun kaure da fada , adaidai suna kokuwa sai ta yanke jiki ta fadi kasa ta yi mummunar buga kanta a kasa.
” Duk da wannan fadi da matar sa ta yi, ba kyale ta ba sai ya ci gaba da lakada wa matar sa dukan tsiya har sai da ya ji bata numfashi.
Adejobi ya ce Idibie na tsare a ofishin su sannan fannin gurfanar da masu laifuka irin haka za ta ci gaba da bincike akai.
A karshe ya gargadi ma’aurata su rika yin hakuri da juna a duk lokacin da wani sabani ya shiga tsakanin su domin gujewa aikata abinda za a yi wa da-na-sani daga baya.
Discussion about this post