Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya, Abuja (FCT), sun bayyana damke wasu karti shida a Apo, wadanda ake zargi da garkuwa da mutane.
Wannan bayani na cikin wata sanarwa da Kakakin Yada Labarai ta FCT, Mariam Yusuf ta fitar a Abuja, a ranar Lahadi.
Mariam ta ce an kama wadanda ake zargin bayan wata kwakkwarar majiya ta gulmata mata cewa akwai alamomi da ke nuna cewa mutanen suna rike da wasu mutum uku da su ka yi garkuwa da su.
An kama su kamar yadda ta bayyana a lokacin da jami’ai ke sintiri, su kuma wadanda ake zrgin a lokacin sun a kokarin canja wa daya daga cikin wanda su ka yi garkuwa da shi wurin da za su sake boye shi.
Ta ce daga nan bincike ya sa an gano wasu mutane biyu da masu garkuwar ke rike da su.
Bayan an kamo su an kais u ofishin ‘yan sanda inda aka tsare wadanda ake zargin su shida, wadanda aka yi garkuwar da su duk sun shaida cewa su din ne su ka kamo su.
Daga nan Mataimakiyar Sufurtanda Mariam ta ce hukumar ‘yan sandan Abuja ta kaddamar da gagarimar rundunar dakile ayyukan garkuwa da mutane a Abuja da kewaye.
Sannan kuma rundunar na aiki kafada da kafada da sauran hukumomin tsaron domin tabbatar an samu kyakkyawan tsaro a yankin.
Ta kara yin kira ga jama’a su kwantar da hankulan su, su kasance masu bin doka, kuma su rika kai rahotonduk wani da ake zargin batagari ne a cikin su.
Ta bada lambobin da mazauna Abuja da kewaye za su iya kira kamar haka: 08032003913, 08061581938, 07057337653 and 08028940883.