’Yan jagaliya sun kashe wani jigon jam’iyyar APC

0

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Benuwai ta bada sanarwar kisan gillar da aka yi wa Tersoo Ahu, Shugaban Jam’iyyar APC na mazabar Gboko ta Kudu, cikin Karamar Hukumar Gboko.

Rundunar ta kuma tabbatar da cewa wasu ’yan iskan gari ne su ka kashe dan siyasar.

Kakakin Rundunar ta Jihar Benuwai, Catherine Anene, ta tabbatar da wannan bayanin kisa ga manema labarai a Makurdi, babban birnin jihar Benuwai a ranar Lahadi.

Anene ta kara da cewa binciken farko ya tabbatar da cewa wasu ’yan iskan gari na cikin jam’iyyar APC ne masu adawa da shugaban jam’iyyar su ka kai mara hari a cibiyar da ake sabunta rajistar APC.

Anene ta kara da cewa mamacin da wasu ‘yan jam’iyyar APC na wurin bayar da horon sabunta rajista da tantancewa ne a lokacin da ‘yan jagaliyar su ka dira wurin dauke da makamai.

Rundunar ta kara cewa wani dan iskan gari ya kwantsama wa shugaban jam’iyyar falankin katako bisa kan sa, inda ya kife kasa a kwance.

Ana zuwa asibiti kuma aka tabbatar ya mutu.

“Matasan da ke ikirarin ‘yan daga bangaren jam’iyyar APC ne, sun hada gangami su ka kai hari kan mamacin da sauran wasu ‘yan siyasa a inda ake bayar da horon sabunta rajistar APC a rumfar zaben mazabar.

“Sun yi ikirarin cewa ba a wurin ba ne aka amince za a yi horaswar sabunta rajista, shi ya sa su ka nemi hana yin horaswar a wurin.

“Sun dira wurin da duwatsu, katakai, da sanduna, su ka rika anytaya jifa kuma wani daga cikin su ya faskara wa shugaban jam’iyya a mazabar falankin katako bisa kai. Ya kife a kasa ya fadi.”

Anene ta ce baya ga kisan da aka yi, an kuma ji wa wasu dama raunuka.

Share.

game da Author