Masu garkuwa da ke rike da wakilin jaridar PUNCH mai suna Okechukwu Nnodim a Kubwa, Abuja sun nemi a biyan kudin fansa har naira milyan 10 kafin su sake shi.
Sun kutsa har cikin gidan sa a Kubwa, ranar Alhamis da dare su ka tafi da shi, tare da wasu ‘ya’yan makautan sa biyu.
Matar sa Oluchi Nnodim ta shaida cewa kafin su kutsa cikin gidan sai da su ka rika harba bindigogi a sama kuma cikin gidan sun rika harbin daya daga cikin tagogin dakin gidan.
Ta kara da cewa daga baya sai suka yi amfani da karfi su ka balle kofar tagar da kafaran da aka kafa a kofar.
“Miji na ya ce min kada na fito na tsaya tare da yara. Daga nan sai na ji ana tambayar sa cewa ya fito da kudin da ya ke da su. Ya shaida masu ba shi da ko sisi.”
Ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa masu garkuwar su biyar ne, kuma kowanen su dauke da bindigogi.
Sai dai kuma ta ce ba za ta yi maganar komai ba, domin su na magana da wani kan batun kokarin sakin mijin na ta.
Sai dai kuma wata ruwaya ta tabbatar da cewa wata ’yar uwar sa da ke Lagos ta ce masu garkuwar sun nemi a biya su naira milyan 10 kafin su sake shi.