‘Yan bindiga sun yi wa kungiyar kwallon kafan Adamawa United fashi, sun sace direban motar

0

‘Yan fashi sun yi tare motar ‘yan wasan kungiyar kwallon fata na Adamawa United a hayar zuwa Legas domin wasan su da MFM ranar Lahadi.

Barayin sun kwace musu komai na su harda kudaden abinci da na Otel da kuma wayoyinsu.

Bayan haka sun waske da direban motan.

‘Yan bindigan sun tare motar a hanyar Benin zuwa Legas da karfe 11.30 na daren Asabar.

PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda kungiyar kwallon kafan ke fama da rashin kudi wanda na abinci ma yakan gagare su wataran.

Yadda Adamawa United ta makale a Bauchi saboda rashin kudin isowa Kaduna wasan su da Jigawa Golden Stars

PREMIUM TIMES ta gano cewa yan kwallon sun makale ne a Bauchi ne saboda rashin kudin man da zai kawo su Kaduna sannan ka dan karan yunwa da suke ji babu kudin abinci.

” Muna cikin tsananin wahala, duk da cewa gwamnatin jihar na ba kungiyar naira miliyan 12.5 duk wata domin kula da su da kuma tafiye tafiyen mu amma ba su isowa gare mu. Tun da aka raba mana naira N5000 a makonni biyu da suka wuce muci abinci bayan wasn mu da Rivers, ba a sake bamu komai ba sai kwanaki suka bamu nair N2500 mu ci abinci.

” Tsakani da Allah muna wahala ne kawai a Adamawa United, domin muna buga kwallo ne cikin babu abinci. gangandawa kawai muke yi. Ko daga Yola wani ne masoyin kwallo mutumin arziki ya biya mana kudin mota sannan ya biya mana kudin Otel na kwana biyu a Bauchi ” Haka wani dan wasa ya shaida wa PREMIUM TIMES.

Adamawa United ce ke karshe a tebur din kwallon kafa na rukunin kwararru a Najeriya.

Share.

game da Author