Jami’an ‘yan sanda sun damke wata mata mai suna Tini Essi, da ke kan titin Orijamogun, Ikorodu a Legas, saboda zargin kisan dan-haya mai suna Christian Akparie, mai shekaru 49.
Kakakin ‘Yan Sandan Jihar Legas Olumuyiwa Adetobi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a ranar Laraba.
Essi wadda ‘yan mai gidan hayar ce, ta yi rigima da daya daga cikin ‘yan hayar gidan a kan kudin wuta, kafin rasuwar mamacin.
Rigimar ta faru a ranar 31 Ga Janairu, 2021, shi kuma dan-hayar ya mutu a ranar 6 Ga Fabrairu, bayan ya sha jiyyar dukan da Essi ta lakada masa.
“Binciken farko da jami’an tsaro su ka gudanar ya tabbatar da cewa a ranar 3 Ga Janairu, 2021, an yi sa-in-sa tsakanin su a kan biyan kudin wuta. Wannan sa-in-sa ta kai su ga fada tsakanin su.
“Bayan fadan, mamacin kafin rasuwar sa ya rika fama da tsananin ciwo wanda ya samu sanadiyyar dukan da Essi ta yi masa. Amma a ranar 6 Ga Fabrairu ya mutu a lokacin da ake kan hanyar garzayawa da shi babban asibitin Ikorodu.” Hakan na kunshe cikin bayanin ’yan sanda.
Adejobi ya ce wannan ya sa jami’an ’yan sandan da ke aiki da dibijin na Ikorodu su ka damke wadda ta lakada masa dukan da ya yi sanadiyyar tafiyar sa lahira.
Kwamishinan ‘Yan Sanda Hameed ya yi kira ga dangin mamacin su yi hakuri su taushi zukatan su, kada su dauki dokar ramuwar-gayya a hannun su.
Ya ce ‘yan sanda za su tabbatar da an bi wa mamacin hakkin kisan da aka yi masa.
Tuni dai Kwanishinan ‘Yan Sanda ya sa aka maida wadda ake binciken a babban ofishin bincike na CIB da ke Panti, Legas.
Discussion about this post