Yadda ‘Yan bindiga suka kashe mahaifi da dansa a Igabi, jihar Kaduna

0

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana yadda mahara suka kashe mahaifi da dansa a karamar hukumar Igabi.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Gida, Samuel Aruwan ya sanar da haka ranar Lahadi a garin Kaduna.

Aruwan ya ce jami’an tsaro sun sanar wa gwamnati cewa maharan sun far wa kauyen Baka a daren Asabar ne.

“Maharan sun kashe mahaifi da dansa daya sannan sun sace mutane da dama daga wannan kauyen wanda mafiyawansu mata da yara kanana ne.

“Jami’an tsaron dake garin Sabon Birni sun yi arangama da maharan inda suka yi nasaran ceto wasu daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su.

Gwamnan jihar Nasir El-Rufa’i ya yaba kokarin da jami’an tsaron suka wadannan mahara da kuma ceto wasu daga cikin mutanen da maharan suka yi garkuwa da su.

Share.

game da Author