Sahihan bayanan da PREMIUM TIMES ta kara samu, sun nuna yadda sojojin Najeriya su ka yi gagarimar nasarar markade mayakan Boko Haram, tare da yi masu luguden-wuta, sannan su ka kwato garin Marte daga hannun ‘yan ta’adda.
Garin Marte ya kasance a hannun Boko Haram tsawon mako guda cur, kafin zaratan Najeriya su yi galabar kwato garin.
Ranar Talata ce sojojin Najeriya su ka bada sanarwar kwato karamar hukumar Marte daga hannun Boko Haram.
Kakakin Yada Labarai na Sojojin Najeriya, Mohammed Yerima ne ya yi sanarwar, kuma ya aika wa kafafen watsa labarai.
Wasu sahihan bayanai da PREMUM TIMES ce kadai ta samu, sun nuna yadda sojojin Najeriya su ka yi shirin kakkabe Boko Haram a Marte, kuma su ka yi nasara.
Tun da farko dai sojojin Burged din Musamman ta 402 su ka darkaki Karamar Hukumar Marte da misalign karfe 8 na safe, a ranar 23 Ga Fabrairu, bayan sun yi kyakkyawan shiri.
Yayin da zaratan sojojin Najeriya su ka kusa Marte, wajen karfe 2 na rana, sun rika cin karo da nakiya a kan hanya, wadda Boko Haram su ka rika binnewa.
Sojojin Najeriya sun yi nasarar tonewa da kuma kwance duka nakioyi tara da su ka ci karo a su a kan hanya, wadanda aka turbude a niyyar kashe sojojin.
Majiyoyin PREMIUM TIMES sun bayyana cewa yayin da sojojin Najeriya su ka kutsa cikin garin Marte, Boko Haram sun rika yin harbin-kan-mai-uwa-da-wabi, amma sojojin Najeriya su ka dake, su ka rika yi masu luguden-wuta.
An shafe sa’o’i da dama ana zabarin wuta, inda sojojin Najeriya su ka kashe Boko Haram 19, wasu da dama kuma su ka tsere da raunuka a jikin su.
Yayin da Boko Haram ke guduwa, su kuma sojojin Najeriya sun rika rera wakokin nasara
Daga cikin kayan da aka kwato daga Boko Haram, akwai bindiga samfurin AK 47 guda bakwai, mota samfurin Hilux guda guda biyu da kuma bingidar harbo jiragen yaki biyu, wadanda aka girke kan motocin Hilux din guda biyu.
Sannan kuma an yi raga-raga da manyan motocin yaki na Boko Haram guda biyu.
Yanzu dai Marte da kewaye na zaman kwanciyar hankali. Kuma sojoji sun nuna jajircewa da kokarin da tabbas sun cancanci a yaba masu.
PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda Boko Haram su ka kashe sojoji 17 a harin kwanton-bauna da su ka kai wa sojojin a sansanin Marte.
Wannan harin ne ya sa aka kwashe sauran sojojin zuwa sansanin Dikwa, domin tsara yadda za su kwato Marte daga hannun Boko Haram.
A ranar Talata sai Kakakin Yada Labarai na Rundunar Sojojin Najeriya, Mohammed Yerima, ya bayyana cewa sojojin Najeriya sun kwato Marte daga hannun Boko Haram, tare da taimakon sojojin sama.
Daga 2011 zuwa yau dai Boko Haram sun kashe kosun haddasa mutuwar sama da rayukan mutum 37,500, kamar yadda Ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai lura da Harkokin Agaji ya tabbatar.
Sannan kuma an kiyasta cewa sama da mutum milyan 2.5 ne su ka rasa muhallin su.
Har yau kuma dubban daruruwa na zaman gudun jihira a sansanoni daban-daban a Jihar Barno, wasu jihohi da makwautan kasashe.
Discussion about this post