• PREMIUM TIMES |
  • Tallata Hajar ka |
  • Adireshin mu |
  • PTCIJ |
  • Dubawa
Premium Times Hausa
  • Labarai
    • All
    • Duniya
    GANAWAR TINUBU DA NLC: Ƙungiyar Ƙwadago ta ce a tilas a soke ƙarin kuɗin mai, an shammaci ‘yan Najeriya

    Buhari-signing-2020-budget

    Gwamnatin tsohon shugaban kasa Buhari ta sanar da sabbin nade-nade a daidai ana rantsar da Tinubu shugaban kasa

    Minista Sadiya ta miƙa ragamar Ma’aikatar Harkokin Jinƙai ga Babban Sakatare

    2015-2023: ‘Na yi sukuwa ta lafiya, na kai zamiya lafiya’ – Buhari

    BANKWANA DA BUHARI: ‘Tinubu yau mafarkin ka ya zama gaskiya, Allah ya sa ka kai Najeriya fiye da inda na kai ta’ – Nasihar Buhari ga Asiwaju

    Tsakanin Sanata Barau da Gwamna Ganduje, Daga Jaafar Jaafar

    Ba zan jira Litinin ba, tun Lahadi zan mika mulki ga Abba Gida-Gida in kama gaba na – Ganduje

    RANTSAR DA TINUBU: Kotun Koli ta yi watsi da karar rashin cancantar Tinubu shiga zaɓen 2023

    RANAR RANTSAR DA TINUBU: Za mu hana makiyaya karakaina da shanu a cikin Abuja – Shugaban Miyetti Allah

    An Karrama gidan Jaridar PREMIUM TIMES da kyauta mafi daukaka a aikin Jarida na kasar Amurka

    BA DA MU BA, TAYA ƁERA ƁARI: PREMIUM TIMES ta nesanta kan ta daga ƙungiyar da ta jona sunan ta a shirya taron karrama wasu mutane

    KIRAN RUWA: ‘Ka wa Allah ka ɗaga mana kafa, kada ka kwace mana filayen mu har 9 da ka kunno kai a kan su – Makarfi ga El-Rufai

  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
    TSOHO MAI RAN ƘARFE: Obasanjo ya zura ƙwallaye uku a wasan sada zumuntar tsoffin ɗaliban sakandare

    QATAR 2022: Yadda Croatia, ƙasa mai mutum miliyan 4 ta kori Brazil ƙasa mai mutum miliyan 216

    AMBALIYAR QATAR 2022: Spain ta kori kociya Luis Enrique bayan ta kwashi buhun kunya a hannun Marocco

    QATAR 2023: Yadda Walid, kociyan Morocco ya rikita duniyar ƙwallon ƙafa cikin watanni 4 kacal

    QATAR 2022: Dukkan ƙasashen Afrika 4 da su ka taɓa kai wasan kaiwa ga na kusa da na ƙarshe, su na da tauraro a jikin tutocin su

    Abubuwan al’ajabi dangane da fatattakar da Morocco ta yi wa Spain daga Qatar 2022

    QATAR 2022: Ko ƙasashen Afrika za su fidda nahiyar jin kunya a duniyar ‘yan ƙwallo

    DAGARGAZA ARGENTINA: Ƙasar Saudiyya ta ba da hutun kwana Ɗaya a wataya

    QATAR 2022: 2:1: Saudiyya ta kafa tarihin karya gadara da tutiyar buga wasan Agentina 36 a jere babu rashin nasara

  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna
    Buhari ya tashi zuwa Saudiyya, zai yi Umra ta ƙarshe a matsayin sa na shugaban kasa

    BIDIYO: Buri da fata na a 2023: Ra’ayoyin jama’a

    BIDIYO: Ƙogon Al’ajabi, ƙogon Waraka, Ƙogon biyan bukata a jihar Enugu

    Mutanen Arewa na da alƙawari da sanin ya kamata, Tinubu za su yi saboda ƙauna da biyayyar da ya nuna wa Buhari – El- Rufai

    BIDIYO: NAJERIYA @62: Ra’ayoyin ‘yan Najeriya game da mulkin Buhari a tsawon shekaru 7 da suka gabata

    Buhari bai san ƴan ta’adda sun fidda bidiyon da suka ce sai sun sace shi da ni ba sai da na ziyarce shi – El-Rufai

    Dalilin da ya sa na raɗa wa wasu fitattun gine-gine, da titunan jihar Kaduna sunayen wasu fittattun ƴan asalin jihar

    HOTUNA: Ɗan Autan marigayi tsohon sarkin Kano Ado Bayero, Mustapha Ado Bayero, ya auri mata biyu ranar Asabar a  Kano

    BIDIYO: An yi wa ɗan takarar mu murɗiya a zaɓen fidda gwani na APC a Legas – Masu zanga-zanga

No Result
View All Result

Yadda Shirin Sabuwar Hanyar Bada Karatu zai magance rashin zuwan yara makaranta – Minista Sadiya

Ashafa MurnaibyAshafa Murnai
February 16, 2021
in Labarai
0
Kwasar Kayan Tallafi: To yanzu sai mu daina zagin Minista Sadiya, Daga Mohammed A. Mahmood

Kwamitin Gudanarwa kan Shirin Sabuwar Hanyar Bada Karatu (National Steering Committee on Alternate School Programme) ya yi taron sa na farko a ranar Litinin a Gidan Ma’aji (Treasury House) da ke Abuja.

Taron ya fara aiwatar da tsare-tsare kan hanyoyin da za a bi a magance matsalolin da ke sanya yara su daina zuwa makaranta a Najeriya tare da gaggauta rage yawan irin waɗannan yaran ta hanyar sama masu ilimin farko mai inganci da ilimin sana’o’in a wasu yanayi na musamman waɗanda ba a magance su a tsarin da ake da shi a yanzu ba.

A jawabin ta na buɗe taron, ɗaya daga cikin shugabanni biyu na kwamitin, kuma wadda ta kira taron, Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Sadiya Farouq, ta bayyana cewa Najeriya ce a sahun gaba na ƙasashen da ke da yaran da ba su zuwa makaranta a duniya, wanda hakan ne ya sa Gwamnatin Tarayya ta fito da dabarun musamman ta hanyar ƙaddamar da wannan Kwamitin Gudanarwan kwanan nan.

‘Najeriya Ta Fi Kowace Kasa Yawan Yaran Da Ba Su Zuwa Makaranta’ – Minista Sadiya

Ta ce: “Sanin ku ne cewa Nijeriya ce ƙasar da ta fi kowace ƙasa a duniya wajen yawan yaran da ba su zuwa makaranta. Saboda haka ne Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da Shirin Musamman na Tsara Zuwa Makaranta (ASP) domin tabbatar da cewa kowane yaro da bai zuwa makaranta a Nijeriya ya samu hanyar samun ingantaccen ilimin farko, ba tare da nuna masa bambancin wajen zama, al’ada ko matsayin tattalin arziki ba.

“Ana sa ran cewa Shirin Musamman na Tsara Zuwa Makaranta zai taimaka wajen samar da damammaki ga yaran da ba su zuwa makaranta don su samu ƙwarewar da za ta tallafi rayuwar su daga koyarwar sana’o’i da kasuwanci da za a yi masu domin su amfani al’umma.

“Kowanne daga cikin membobin wannan Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa an zaɓe shi ne cikin tsanaki a cikin tunanin ɗimbin gudunmawar da zai kawo wajen fito da hanya mafi dacewa da za a bi a wannan shiri.”

An tsara Shirin Musamman na Tsara Zuwa Makaranta ne don ya inganta hanyar da za a samar da ilimi ga dukkan yaran da ke Nijeriya kamar yadda Shirin Kyautata Rayuwa (SDG-4) ya tanada kan samar da ingantaccen ilimi ga kowa da kowa kuma ya rage yawan yaran da ba su zuwa makaranta ƙwarai da gaske ta hanyar gwama tsarin karatun aji da wanda ba na shiga aji ba.

Manufar sa ita ce ya kawar da ko kuma ya rage yawon banza matuƙa, barace-barace na ƙananan yara, sannan ya haɓaka zaman lumana, haɗin kai da tattaro yara wuri guda daga sassan rayuwa daban-daban.

Ayyukan da aka ba ‘yan kwamitin sun haɗa da tabbatar da tsare-tsaren shirin na ASP sun fara aiki sosai a duk faɗin ƙasar nan, su ƙara goge tare da tsara manufar shirin, su duba kowane aiki tare da amincewa da shi, kuma su aiwatar da tsare-tsare tare da yin duk wani aiki da zai inganta aiwatar da shirin.

Kwamitin mai membobi 17 ya na ƙarƙashin shugabancin Minista Sadiya da Ministan Ilimi Malam Adamu Adamu.

Sauran ‘yan kwamitin su ne Ƙaramin Ministan Ilimi, da Babban Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan SDGs, da Ƙaramin Ministan Kasafi da Tsare-tsaren Ƙasa, da Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa, da Babban Sakataren Hukumar Bada Ilimin Farko (UBEC), da kuma wakilan (UNESCO) da (UNICEF) da ‘Global Partnership for Education’.

Sauran su ne shugaban ƙungiyar mashawarta kan sana’o’i masu zaman kan su (SDGs) da shugaban haɗakar mashawarta masu zaman kan su kan cigaban ƙasa, da shugaban Kwamitin Ilimin Farko a Majalisar Dattawa, da shugaban Kwamitin Ilimin Farko a Majalisar Wakilai, Hon. Dr. Shehu Balarabe Kakale, da Darakta Janar na NYSC, da kuma Babban Sakatare a Ma’aikatar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa Bashir Nura Alƙali a matsayin Sakatare.

Tags: AbujaFarouqHausaKaratuLabaraiNajeriyaNews
Previous Post

Abdulrasheed Bawa, sabon shugaban hukumar EFCC

Next Post

‘Ka cika surutu, ka bi Gwamnan Kwara ka zauna lafiya – Shawarar APC ga Lai Mohammed

Ashafa Murnai

Ashafa Murnai

Next Post
Lai Mohammed

‘Ka cika surutu, ka bi Gwamnan Kwara ka zauna lafiya – Shawarar APC ga Lai Mohammed

Binciko

No Result
View All Result
Karanta

Ramadan Kareem AD

Sabbin Labarai

  • SHARI’AR ZAƁEN SHUGABAN ƘASA: Tinubu da INEC sun ƙi amincewa da tulin kwafe takardun da Atiku ya kwafo daga iReV
  • GANAWAR TINUBU DA NLC: Ƙungiyar Ƙwadago ta ce a tilas a soke ƙarin kuɗin mai, an shammaci ‘yan Najeriya
  • HAJJI 2023: Gwamnatin Filato ta bar mahajjatan jihar su na hajijiya a Madina
  • Kada ku tausaya min don na faɗi zaɓen Sanatan Zamfara – Sanata Marafa
  • JIRAN TSAMMANI: Tinubu zai saka wa waɗanda su ka yi wa APC hidima da waɗanda su ka wahala saboda jam’iyya – Marafa

Abinda masu karatu ke fadi

  • auto verkopen on ZAMFARA: Mahara sun gudu sun bar bindigar harbo jiragen sama a dajin Gumi da Bukkuyum -Inji ‘Yan Sanda
  • Laser-Haarentfernung mit hygienischen Bedingungen und aktuellen Gesundheitsstandards in der Türkei on An yi min murɗiya ne a zaɓen APC, ban yarda ba sai an sake zaɓe – Korafin Bashir Ahmad
  • Call Girls Sehore on Ƙungiya ta yi kira ga gwamnati ta ware kuɗaɗe domin samar da dabarun bada tazarar Iyali
  • buy aged stripe account on Hukumar NBC ta gayyaci mai gabatar da shirin ‘Berekete’, bayan macen da ta kona gashin kan yarinya barkatai, ta sha mari barkatai a hannun sa
  • research and survey on Gwamnan Edo ya bijire wa umarnin kotu, ya ce sai mai shaidar rigakafin korona zai yi sallar jam’i a masallaci

Fanni

Tweets by PTimesHausa
  • All Homepage Blocks
  • Home
  • Home
  • Main Home

© 2023 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.