Kotu a Mapo dake Ibadan jihar Oyo ta raba auren wata mata da mijinta mai suna Ebun na tsawon shekaru 17 da mijinta Ismaila Adams saboda rashin zaman lafiya a tsakanin su.
Alkalin kotun Ademola Odunade ya baiwa Ebun ‘ya’ya biyun da suka haifa ta ci gaba da rike su da kuka da su sannan shi kuma mijin nata zai rika aika mata da naira 10,000 duk wata kudin kula da ‘ya’yan.
A zaman da kotun ta yi ranar Litini Adams ya roki kotu da ta raba wannan aure saboda matar sa Ebun na son ta kashe shi.
Ya ce Ebun kan rarrumi wuka ko kwalba ta nemi ta nemi luma masa idan sun sami wani sabani a tsakanin su.
“Ya kai ga dole na fice na bar mata gidan da muke a ciki saboda tsoron kada ta ga baya na.
ita ma matar ta amince a raba wannan aure tana mai cewa Ismaila kasurgumin mashayin giya ne.
” Sai ya je ya yi tatil da giya sannan ya ke dawo min gida, kuma a wannan rana babu abinda yake yi mini illa ya lakada mini dukan tsiya da yi mini zagin fitar arziki ta uwa ta uba.
A karshe bayannan su dai Kotu ta raba auren kowa ya kama gaban sa.