Idan ba a manta ba a daren Asabar din makon jiya an ruwaiyo yadda wasu mahara suka far wa kauyen karamar hukumar Igabi, jihar Kaduna, suka kashe mahaifi da dansa.
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Gida, Samuel Aruwan ya sanar da haka inda ya ce jami’an tsaro sun sanar wa gwamnati cewa maharan sun far wa kauyen Baka kuma sun sace mutane da dama wanda mafi yawan su mata da yara kanana ne.
A ranar Lahadi ma, wato jiya, wasu ƴan bindigan sun kai hari a kauyen Kikwari dake karamar hukumar Kajuru, a nan kuma sun kona wani babban cocin Holy Family Catholic Church’ da gidaje biyu.
Kwamishina Aruwan, wanda shine ya fitar da sanarwar ranar Litini, ya ce maharan basu arce da koda mutum ɗaya daga wannan kauye ba.
“Mazauna kauyen sun gudu daga gidajen su a lokacin da suka samu labarin zuwan maharan.
Gwamnan jihar Nasir El-Rufa’i ya ce gwamnati za ta ci gaba da kokari wajen kawo karshen ayyukan ƴan bindiga a jihar.
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin cewa gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i ya bayyana cewa muddun ba a samu hadin kai tsakanin gwamnonin yankin Arewa Maso Yamma ba, ba za a kawo karshen hare-haren ‘yan bindiga ba.
El-Rufai ya kara da cewa bashi da ra’ayin ayi sulhu da ‘yan bindiga, amma wasu gwamnonin yankin basu son haka ba.
Suna ganin yin sulhu da ‘yan bindigan zai kawo karshen hare-haren.