Yadda Kungiyar Hisbah ta kama kwalaben giya sama da 200 a Bauchi

0

Hukumar Sa-ido Kan Hana Laifukan Da Suka Saba Shari’ar Musulunci (Hisbah), ta bayyana cewa ta kama kwalaben giya 260 a jihar Bauchi.

Kwamishinan Hisbah da tsananta kiyaye dokokin shari’a Aminu Balarabe ya sanar da haka a garin Bauchi ranar Talata.

Balarabe ya ce Hisbah ta kama kwalaben giya 216 a karamar hukumar Misau kuma ta kama wasu kwalaben giya 44 a kulob da gidajen siyar da barasa dake ‘Dass park’.

Ya ce nan ba da dadewa ba kungiyar za ta nemi izinin kotu domin fasarfasa kwalaben barasan da ta kama.

Balarabe ya ce kungiyar ta kama mutum shida dake da gidajen siyar da giya a jihar.

“Bisa ga dokar shari’a da aka kafa a jihar Bauchi a shakarar 2003 wuraren da ake siyar da gijya a jihar sune barikin sojoji ne da na ‘yansanda kawai. Bayan nan babu wani wuri da aka yarda a rika saida barasa a fadin jihar.

” Saboda haka jungiyar hisba na ja wa mutane kunne, duk wanda aka kama yana saida giya zai dandana kudar sa.

Bayan haka wani jami’in kungiyar Aminu Idris ya bayyana cewa a kwanakin baya kungiyar ta kama wasu matasa dake shirya liyafar yin fasikanci da’yan mata a jihar, liyafar mai suna ‘Gwaidu’.

Idris ya ce ana shirya Gwaidu ne domin a rika lalata da ‘yan mata tare da tilasta wadanda suka ki amincewa.

Ya ce kungiyar ta kama iyayen yaran dake hada irin wannan liyafa domin su sa hannu a takarda cewa ‘ya’yan su ba za su sake hada liyafa irin haka ba.

Idris ya yi kira ga gwamnati da ta mai da kungiyar hukumar sannan ta ware mata kudade domin inganta aiyukkan da suke yi a jihar.

Share.

game da Author