Shugaba Muhammadu Buhari ya na tsoffin Hafsoshin Tsaron Kasa, wadanda ya tube cikin makon jiya, a matsayin Jakadu-marasa gafaka.
Ya tura sunayen su ga Majalisar Dattawa a ranar Alhamis domin neman amincewar Majalisa.
Cikin wata wasika ga Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, Buhari ya bayyana cewa “ys zabe su ne tare da neman iznin Majalisar Dattawa, kamar yadda Sashe na 71 (1), (2) (c) da Karamin Sashe na (4) na Kundin Najeriya da aka yi wa kwaskwima na 1999 ya tanadar.”
An nada su mukaman jakadun ne bayan sun sauka da daidai lokacin da aka kosa a sallame su.
Jama’a da dama sun sha bai wa Buhari shawara ya tsige su, ganin yadda matsalar tsaro.
Wani babban gata da Buhari ya yi wa su Buratai, shi ne sanarwar da Gwamnatin Tarayya ta bayar ta bakin Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed cewa, Gwamnatin Najeriya ba za ta binciki su Buratai ba.
Ya ce ya na neman a amince da sunayen Janar Mai Ritaya G Olonisakin, Mai Ritaya Laftanar Janar Tukur Buratai da sauran manyan Hafsoshin wadanda su ka yi ritaya a makon da ya gabata.