Shahararren bankin nan na Amurka mai suna Citibank, ya dibga asarar dala milyan 500 wadanda ya tuttura wa wasu kamfanoni a bisa kuskure.
Kamfanonin dai su ne ke bai wa kamfanin kayan shafe-shafe da kwalisa, wato Revlon ramcen kudade domin hana kamfanin durkushewa.
Da ya ke Citibank ne ejan na Revlon, ya yi niyyar tura wa kamfanonin zuba jarin kudin ruwa na dalar Amurka milyan 7.8.
An tafka babban kuskure aka tuttura masu dala milyan 893, cikin shekarar da ta gabata.
An yi dace wasu kamfanonin sun maida jimillar dala milyan 400, amma saura kamar su 10, sun yi mirsisi su ka ki maida kudin.
Hakan ya fusata shugabannin Citibank har su ka maka kamfanonin bada lamunin kotu, a cikin watan Agusta, 2020.
Sai dai kuma Mai Shari’a Jesse Furman na Kotun Gundumar Amurka, ya yi abin da Hausawa ke kira ‘shari’a sabanin hankali, inda ya zartas da hukuncin cewa babu wata hujjar da za a tuhumi kamfanonin zuba jarin har a ce su maida kudaden.
Wannan hukunci dai ya bai wa mujallar Forbes mai bin diddigin hada-hadar kudade ta duniya mamaki matuka.
Forbes ta ce lallai Citibank ya tafka babban kuskuren da a tarihi babu wani bankin da ya taba tafka irin sa.
To amma kuma Kakakin Yada Labarai na Citibank, ya bayyana hukunci da cewa shiririta ke kawai alkalin ya yi, domin bankin zai daukaka kara.
Ya ce babu yadda za a ce don a tura maka kudi a bisa kuskure su zama na ka.