Hukumar EFCC ta shaida wa Babbar Kotun Tarayya ta Abuja cewa Faisal dan Abdulrashid Maina, wanda ake tuhuma a kotu tare da mahaiin na sa, ya gudu zuwa Amurka.
Lauyan EFCC mai suna Mohammed Abubakar, kuma wanda ya shigar da karar a madadin EFCC, ya ce Faisal ya tsere, a daidai lokacin da kotun ke tuhumar sa da laifukan harkallar karkatar da kudade har tuhumomi uku, shi da mahaifin sa.
Lauyan ya ce EFCC ta samu labarin cewa Faisal ya tsere zuwa Amurka, inda ya bi ta kan iyakar Jamhuriyar Nijar.
Kafin haka dai a ranar Alhamis sai da Mai Shari’a Okon Agbang ya umarci Dan Majalisar Tarayya, Sani Dangaladima, wanda ya karbi belin Faisal cewa ya damka wa kotun kadarorin sa da ya jingina wa kotun a matsayin sharadin karba belin Faisals.
Shi dai Dangaladima, wanda shi ke wakiltar Karamar Hukumar Kaura Namoda ta Jihar Zamfara, ya rattaba amincewar karbar belin Faisal kan kudi naira milyan 60.
Shi ma Maina sai da ya yi kokarin tserewa zuwa Amurka, amma aka damke shi a cikin Jamhuriyar Nijar.
A halin yanzu EFCC ta ki amincewa da sake bada belin Maina, saboda ya na da katin zama dan kasar Amurka.
Ta ce tunda ya yi kokarin gudu a watannin baya, a yanzu ma idan aka bayar da belin sa, sake gudu zuwa Amurka zai yi.