Ya dace Gwamnatin Tarayya ta biya diyyar barnar da Fulani makiyaya su ka yi wa manoman – MURIC

0

Kungiyar Kare Hakkin Musumi ta Najeriya (MURIC), ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ta biya diyyar amfanin gonar da makiyaya su ka cinye wa manoma a fadin kasar nan.

Kungiyar ta bayyana haka a cikin wata sanarwar da ta fitar, wadda Daraktan MURIC Ishaq Akintola a ranar Juma’a.

MURIC ta bayar da shawarar gwamnati ta rika biyan kudin tsilla-tsilla, ba a lokaci daya ba. Amma kuma a tabbatar da cewa manoman da aka yi wa barnar kudaden na zuwa hannun su.

MURIC ta yi wannan jawabi a daidai lokacin da ake korar Fulani makiyaya daga dazukan wasu jihohin kudancin Najeriya.

“A yanzu dai MURIC na da cikakkar shaidar da ke tabbatar da irin barnar da Fulani makiyaya su ka yi wa manoma, inda su ka dauki tsawon lokaci su na cinye masu amfanin gona. Ciki kuma har ma da yankunan Abuja.

“Gaskiyar magana abin da mu ka tabbatar ya sa mun ji kunya sosai, hakan ya nuna wadannan makiyaya ba abin yi wa kara ba ne.

Kungiyar ta rika kawo misalan yadda makiyaya su ka rika cinye amfanin gonar manoma a jihohin Ogun, Oyo, Kwara da yankunan Abuja.

MURIC na kira ga gwamnatocin jihohi da gwamnatin Tarayya su dauki nauyin biyan diyyar barnar da makiyaya su ka yi wa manoman kasar nan.”

Ta ce babu wata shukar da ta yi a rana daya ta fito a rana daya har ta kosa a rana daya aka cire. Ta ce sai an dauki tsawon lokaci ana kula da amfanin gona, a yi noma, da dauran wahalhalu.

Saboda haka zalunci ne a cinye wa manomin abincin sa ba tare da an biya shin hakkin sa ba.

“Gaskiya manoman da makiyaya su ka yi wa barna sun yi hakuri sosai. Don haka Gwamnatin Tarayya ta biya su hakkin su da gaggawa.

Share.

game da Author