Wani hadarin mota da ya afku a kan hanyar Bauchi Zuwa Gombe, ya yi sanadiyyar mutuwar Ibrahim Abdul’aziz, wakillin Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA).
Motar wadda ta hay ace, an ce mutum biyu su ka mutu a ciki, shi da wata mace.
Abdul’aziz ya taba yin rahoto a jaridar LEADERSHIP, kuma kafin rasuwar sa, ya na yiwa jaridu rahoto daga Yola, jihar Adamawa, ciki har da PREMIU TIMES.
Shugaban Kungiyar ’Yan Jarida ta Jihar Adamawa, Isiaka Dedan, ya shaida wa PREMIUM TIMES rasuwar a wayar da aka yi da shi ranar Juma’a.
“Ya rasu a kan hanyar Alkaleri. Kuma na gano cewa ya je ne halartar daurin aure, a cikin wata motar haya.” Inji Dedan.
Dedan ya bayyana rasuwar Ibrahim Abdul’aziz wani abin bakin ciki ne ga kungiyar ta ‘yan jaridar jihar Adamawa.
Gidan Radiyon Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA), ya bayyana cewa, “Allah ya yi wa wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka Ibrahim Abdul’aziz rasuwa yau jumma’a sakamakon mummunan hatsarin mota.
“Ibrahim Abdul’ziz wanda kafin rasuwar sa ya ke daukowa Sashen Hausa rahotanni daga jihohin Adamawa da Taraba, ya gamu da ajalinsa ne a kan hanyarsu ta komawa gida daga Bauchi inda suke tafi daurin auren abokin sa tare da yayan sa Mai Unguwa.
Abdul’aziz ya na daya daga cikin hazikan wakilan Sashen Hausa da banda rahotanni, loto-loto ya ke jagorantar gabatar da shirye-shirye na musamman a Sashen Hausa.
“Abdul’ziz ya kware a dauko rahotannin da suka shafi rayuwar talaka ta yau da harkokin siyasa da kuma harkokin tsaro.
“Kafin rasuwar sa, Abdul’ziz ya shirya muhawara ta musamman kan siyasa da harkokin mulkin Najeriya da ake gabatarwa a shirin Tsaka Mai Wuya ranar Talata.
Banda Muryar Amurka, Ibrahim Abdul’aziz ya na kuma dauko wa wadansu kafofin larabai da dama labarai da su ka hada da Daily Trust, Premium Times, allAfrica, newscrescue da sauran su.”
Allah ya gafarta masa.