Wadanda su ka yi garkuwa da daliban Kagara na neman kudin fansa a hannun iyayen su

0

Mako daya kenan bayan awon-gaba da daibai 27 da wasu mutum 17 daga Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Kagara da ke Jihar Neja, wadanda su ka yi garkuwa da su sun fara tattauna neman kudin fansa daga hannun iyayen su.

Wannan batu ya yi sabani da jawabin da Gwamnatin Tarayya ta yi cewa ta na tattaunawa da wadanda su ka yi garkuwar, kuma za a sako su ba da dadewa ba.

Wani mai ikirarin shi ne shugaban rundunar masu garkuwa din, an ji yadda ya ke bada umarni da kuma gargadi da barazana, a lokacin da ya ke magana da wakilin iyayen yaran ta tsawon minti takwas.

An watsa tattaunawar ta su a soshiyal midiya, inda kwamandan ya rika zayyana sharuddan cewa ba za a taba samun zaman lafiya a Karamar Hukumar Rafi ba, wato cikin Kagara, har sai an soke ‘yan banga, kuma sun daina kashe Fulani.

Wata majiya ta bayyana wa PREMIUM TIMES cewa Dogo Gide ne ake zantawar ta waya da shi tare da wakilin iyayen daliban da aka sace din.

Majiyar ta ce Dogo Gide ne shugaban ‘yan bindigar Neja, Zamfara da Birnin Gwari ta Jihar Kaduna.

Majiyar ta kara da cewa shi ne ya dauki alhakin fashin da aka yi a wani banki a garin Kagara.

PREMIUM TIMES cikin watan Satumba, 2020 ta buga labarin yadda ‘yan bindiga su ka yi fashi a bankin Kagara, tare da kashe dan sanda daya da wasu mutum biyar.

“Ai ku Hausawa da ku da masu masu ilmin ku, ku ne ku ka janyo mu ka dauki makami. Kun tilasta mu zama cikin daji” Haka ya shaida wa wanda ya ke magana da shi domin neman sako yaran.

“Idan har jihar Neja na neman sulhu a zaman lafiya, to yanzu ne za a yi shi. Tun daga Neja har zuwa Ilorin zan iya hana yara na kai hare-hare. Amma idan ba za a yi sulhu ba, to ko na mutu sauran za su ci gaba da kai hari. Amma kuma zan iya hana a sake kai hari a Kagara, idan har sulhu na gaskiya din za a yi.”

Yayin da ya roki Jihar Neja ta yi koyi da gwamnatin Zamfara wajen kokarin yin sulhu, ya rika cika bakin cewa babu abin da za a iya yi masu.

“Ba za ku iya yi mana komai ba. Da mu ka je Kagara cikin damina mu ka yi fashi a banki, me ku ka yi? Wadannan yara kuma zan iya ci gaba da rike su har nan da shekara daya.”

Yayin da wanda ake tattauna biyan diyya ya bayyana cewa iyayen yaran sun amince za su biya naira milyan daya kowane, dan bindigar ya ce kada a raina masa wayau, sun yi kadan. Ya nemi a ba shi lambobin wayar iyayen kowane yaro ya yi magana da su daya bayan daya.

Kakakin Yada Labarai ta Gwamnan Jihar Neja, Mary Noel-Berje, ta sanar wa PREMIUM TIMES cewa gwamnatin jihar na sane da tattaunawar da ake yi tsakanin masu garkuwa da wakilin iyayen daliban.

Ta kara da cewa ita ma gwamnatin jihar Neja ta hana idon ta barci domin ganin an ceto yaran da sauran wadanda aka kama su tare, daga hannun masu garkuwa da mutane.

A cikin tattaunawar da gogarman ke yi da wakilin iyayen yaran, ya ce duk su na sane da yawan jami’an tsaron da aka jibge a Kagara. Kuma wani daga cikin Kagara ne ke ba su labarin duk abin da ake ciki.

Ya nuna cewa wadannan jami’an tsaro babu abin da za su iya, domin sun kasa shiga cikin daji inda su ke su yi artabu har su kwaci yaran a hannun su.

Share.

game da Author