TSANANIN TSADA DA KARANCIN WAKEN SOYA: Cin Kaji ya kusa ya gagari ƴan Najeriya

0

Farashin waken soya, babban hatsin da ake amfani da shi wajen hada abincin kaji, ya kusan ninki biyu a shekarar da ta gabata, a cewar wani binciken kasuwa da PREMIUM TIMES ta yi.

Binciken ya nuna cewa buhun wake mai nauyin Kilogiram 100 da aka siyar akan N12, 000 ko N13, 000 a shekarar da ta gabata, ya tashi zuwa N24,000 a bana. Abin tashin hankali ne ace wai abinci irin waken soya dake gina jikin mutane da kuma dabbobi yayi tashin gwauron zabi kamar yadda yake yanzu.

Folake Aina, manajan darakta na rukunin gonakin VD&S , ta bayyana matsalolin da aka samu a wata hira da PREMIUM TIMES.

Ta ce: “ Ba za ka samu waken Soya cikin sauki ba yanzu a kasar nan. A duk lokacin da ka buka ci ka siya waken soya sai hankalinka ya tashi saboda tsada, farashin yana hauhawa, kuma batun shi ne, waken soya da masara ne abincin da aka fi bukata wajen hada abincin kaji domin akalla kashi 75 na kayan hadin masara ne da waken soya. Amma a kullum farashin su hauhawa yake yi kusan ninkawa ya ke yi.

Shugaban kungiyar manoman waken soya na kasa, Nafiu Abdu ya ba da shawarar cewa dole ne gwamnatin tarayya ta taimakawa manoma da kayan aiki a daidai lokacin da ake bukatan su. Ya ce dole ne a bai wa manoman kayan noma da tallafi da wuri domin a samu albarka mai amfanin.

Sannan kuma da horas da manoma dabarun ayyukan gona na zamani da kuma wadata su da taki da kayan noma.

Babban darakta, kungiyar masu kiwon Kaji na Najeriya Onallo Akpan ya koka kan karancin waken soya da ke sa yanzu kiwon kaji na neman ya durkushe karkaf.

Ya bayyana cewa tan din waken soya daya da ake sayarwa a kan N160,000 a watan Oktoban shekarar da ta gabata ya tashi zuwa kusan N300,000 a kasa da watanni hudu.

“Mafi yawan gonakin da ake kiwon kaji sun fara durkushe saboda tsadar abincin kaji wanda ke da nasaba da karancin waken soya da masara da ake fama da su.

Sannan kuma ma idan ka yi kiwon saida su sai ya zama matsala, saboda tsada da abincin yake da shi. Kajin tsada suke yi haka kwai.

Share.

game da Author