TSAKANIN SHEIKH GUMI DA ’YAN BINDIGA: Sulhu, Wa’azi da Nasiha Malam Ke Yi, ba karbar makamai ba – Salisu

0

Salisu Hassan ‘Webmaster’, na daya daga cikin ’yan tawagar da ke bin Sheikh Ahmad Gumi a duk lokacin da ya kai ziyarar neman sulhunta ’yan bindiga a Arewacin kasar nan.

A zantawar da ya yi da PREMIUM TIMES HAUSA bayan sun dawo daga ziyarar da su ka kai Dajin Sububu da Dajin Pakai cikin Karamar Hukumar Shinkafi ta Jihar Zamfara, ya bayyana wa wakilin mu yadda aka tsara tafiyar da kuma yadda su key i mahada da garken ’yan bindigar.

Salisu y ace duk ziyarce ziyarcen da Sheikh Gumi ke yi, da shi ake zuwa, in banda wuri daya kadai.

“Da farko Jere aka fara zuwa, sai Gamagari, sai Kidandan. Sai kuma cikin yankin Kagarko, inda mu ka je Kanjala. Daga nan an je wani wuri a bayan Millinium City a Kaduna da ake kira Kan Rafi.

“Ya kamata a fahimci cewa ba kai-tsaye aka tashi ake tafiya ba, akwai wata kungiya da ake kira ‘Gam-Allah Fulani Development Association. To kamar it ace tsakani. Sun san Ardo-Ardo na wuraren da za a je, kuma su ne kusan tsakani.

“Kuma Sheikh Gumi ba zuwa ya ke yi karbar makamai a hannun ‘yan Bindiga ba. Shi ai ya na zuwa ne ya yi masu wa’azi, sulhu, nasiha da kuma raba masu littafan addinin Musulunci.

“Sannan kuma duk inda mu ka je, in banda wuri daya, Malam ya kan aza harsashen gina makaranta da masallaci.

Yadda Mu Ka Shiga Dajin Sububu Da Dajin Pakai Na Zamfara:

“Idan ka bi bayanan da na yi a shafin mu, zaka ga na rubuta cewa wani matashi ne mai suna Alhaji Moyi ya kai mu har wurin, tunda sun ce kada mu je da jami’in tsaro ko daya.

“To shi Alhaji Moyi din nan, sun taba kama shi, ya dade sosai a hannun su. Ba su sake shi ba, har sai da aka kai masu naira milyan 13. Wannan dadewa da ya yi a hannun su, ta sa sun saba shi. Kuma sun amince da shi.” Haka Salisu Webmaster ya shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA.

“Kuma ina so ka fahimta cewa su ‘yan bindigar nan ai mahada ce mu keyi da su. Ba su bari mu je har ainihin cikin inda su ke zaune. Ko wadanda mu ka je cikin Zamfara, sun fito ne kusan kilomita 30 daga sansanin su, muka hadu aka tattauna.”

Salisu dai su ne ke kula da daukar hoto da bidiyo da kuwa watsa bayanan tafiyar Sheikh Gumi.

Ga bayanan da ya watsa bayan komawar su Kaduna daga ziyarar da su ka kai cikin surkukin dazukan da gungun ‘yan bindiga su ka yi kaka-gida a Jihar Zamfara:

“A rana ta biyu, wato ranar 2 Ga Fabrairu,2021 cikin kokarin da Sheikh Ahmad Gumi ya ke yi na ganin Allah ya dawo da zaman lafiya a tsakanin Fulani da jama’ar gari, Malam ya samu damar shiga Karamar Hukumar Shinkafi a Jihar Zamfara.

“Ya kai ziyarar kwanaki biyu da kuma amsa gayyatar Gwamnan Jihar Zamfara, domin ganin kokarin da gwamnatin sa ta ke yi don ganin ta tsugunar da Fulani a inda ta gina musu.

“Bayan da tawagar Malam ta karya da misalin karfe 11 na rana, mun kama hanya sai fadar Sarkin Shinkafi inda mu ka dauki tsawon awa daya da rabi kafin mu kai fadar.

“Isar mu ke da wuya Mai Martaba Sarkin Shinkafi ya fito da tawagar sa su ka karbi Malam hannu bibbiyu, inda da farko aka karanta Alkur’ani Mai Girma daga bakin Alarammomi.

“Sheikh Gumi wanda ya yi cikakken bayanin dalilin zuwan mu wannan gari da kuma nufin sa na shiga cikin daji domin ganawa da kwamandojin dajin don fada musu kalmomin Allah da kuma nuna musu matsayin zubar da jini da kuma hanyoyin da ake fata idan aka bi su Allah zai bada dawwamammen zaman lafiya a masarautar sa.

“A na sa jawabin Sarkin Shinkafi ya yi godiya ga Allahu Subhanahu Wata’ala da Allah ya albarkace su da zuwan Malam da tawagar sa, ya fada wa Malam irin zaman lafiya da aka samu tun bayan zuwan Gwamna Matawalle a matsayin Gwamna, da kuma aminci da Fulani su ke da shi a wannan yanki nasa.

“A na sa jawabin Shugaban Karamar Hukumar Shinkafi, ya yajjada kalaman Sarkin Shinkafi inda ya tabbatar wa da Malam tsawon watanni shida ba su sami rahoton daukar wani ko kashe wani ba saboda irin zaman lafiya da su ke yi da Fulanin yankin sa.

“Sai dai a na sa jawabin ya yi korafi game da yadda ake karya wa Fulanin alkawarin su da kuma rashin samun amincewa idan su ka yarda aka yi sulhu ya bayar da misalin wanda ya ajiye makami daga baya, ya shigo kasuwa hukuma ta kama shi ta kashe.

Ya fadi irin rashin zaman lafiya da garin Shinkafi ya yi a waccan gwamnatin da ta wuce inda ya ce sun biya kudin fansa masa da milyan 197 mun samu marayu sama da 600, mata 373 da suka rasa mazan su.

Sun Ki Yarda Mu Je Da Jami’an Tsaro Ko Daya:

“Gamawar mu ke da wuya sai muka samun tabbacin gayyatar wadannan kwamandojin dajin inda su ka bayar da sharadin cewar motoci biyar ne kawai su ke bukatar shigowa inda su ke. Sannan da sharadin ba su yarda wani jami’i ko daya ya taka dajin na su ba.

“Bayan da aka gama shiye-shiye da zaben wadanda za su yi wa Malam rakiya, mu ka kama hanya inda muka yi tafiya ta akalla kilomita 15-20 kafin isa wurin su.

Bayan Babban Limamin Sultan Bello ya bude taro da addu’a da fatan Allah ya albarkaci abin da da za a tattauna. Malam Nasiru ya gabatar da Malam da tawagar ga Kwamandojin ‘Yan bindiga.

‘Babu Zaman Lafiya Sai An Daina Buge Fulani A Kasuwannin Kauye Da Wurin Kiwo’ – Bello, Kwamandan ’Yan Bindiga

‘A jawabin sa, Bello wanda ya fara da bai wa Malam hakuri game da tsaiko da aka samu kafin su sami damar shigowa ya ce saboda rashin sanar da su a kan lokaci ne. Ya bai wa Malam shawara ga shiryawa sosai da bayar da sanarwa kafin a zo domin su tara na su jama’a sosai.

“Ya yi magana a madaddin kwamandojin dajin, inda ya ce tun daga lokacin da aka zauna da su cikin daji domin yin sulhu ba su karya wannan sulhun ba. Kasancewar wannan sabuwar gwamnatin Zamfara ta fito da wadansu hanyoyi da su ka taimaka wurin kawo zaman lafiya.

“Kwamandan ’ya ce duk irin ci gaba da za a kawo in dai ba za a daina buge Fulani ba a Jihar Zamfara, idan su ka shiga kasuwa ko wurin kiwo, to ba za a samu dawwamammen zaman lafiya ba.

“A na sa jawabin Sheikh Gumi bayan fada musu matsayin addinin Musulunci game da daukar makami a kan musulmai, kuma ya yi masu alkawari game da kai koken su inda ya dace.

“A na sa jawabin, DPO na Karamar Hukumar Shinkafi ya bada tabbacin cewar su na iya kokarin su wurin ganin an kawo karshen wannan matsala ta kashe ’ya’yan Fulani da kuma sasanci tsakanin su da jama’ar gari.

“Shugaban Karamar Hukumar Shinkafi ya yi masu godiya bisa hadin gwiwa da su ke ba wannan gwamnatin da kuma kara tabbatar musu da cewar tunda Malam ya shigo ga kuma abin da gwamnatin Matawalle ta ke yi, in Allah ya yarda za a kara samun zaman lafiya mai dorewa.

“Tun da farko sai da Alhaji Shehu Buba ya fara gabatar da nashi jawabin a harshen Fulatanci da kuma kara tabbatar musu da cewar wannan tafiyar tsakani da Allah ce babu yaudara ko siyasa ya kuma fada musu su na iya kokarin su ga an kawo karshen wannan kashe-kashen da ke faruwa a fadin Arewacin Najeriya baki daya. A karshe Malam ya raba musu littafan Ahalari da Bagadadi domin karantar da su.

‘Duk Wanda Ya Da Dauki Hoton Mu Zan Bindige Shi’ –Kachalla, Kwamandan Dajin Sububu

“Wannan dajin Sububu da mu ka shiga da farko sun hana a dauko komai a bidiyo ko hoto inda Kachalla, daya daga cikin kwamandojin ya ce duk wanda ya dauki hoton su za su harbe shi.

Amma daga bisani Muhammadu Bello ya yarda a dauke shi. Ya ce dama shi ya saba magana a gaban ’yan jarida kuma daman shi ne tsani tsakanin gwamnati da jama’ar Fulani.

‘Shigar Mu Tsakiyar Garken ’Yan Bindiga Sama Da 500 A Dajin Pakai’:

“Fitar mu ke da wuce ba mu zarce ko’ina ba sai cikin kurmin daji, inda mu ka kwashe tsawon mintina 45 mu na tafiya kafin mu kai garin Pakai. Can mu ka samu daba mafi girma da ban-tsoro da ke tsakanin Zurmi da Shinkafi inda su ka tara da samari da matasa ‘yan shekara 14 zuwa 35 sama da 500. Dukkan su babu wanda babu bindiga a rataye da kafadar sa, da kayan sojoji a jikin su.

“Bayan da Shehu Buba ya gabatar Limamin Sultan Bello Kaduna da Sheikh Dakta Muhammad Sulaiman Adam, ya ci gaba da bayyana makasudin shigowar mu wannan dabar inda ya fada musu kokarin da Sheikh Ahmad Gumi ya ke yi na ganin an samu dawwamannen zaman lafiya.

‘An Talauta Fulani, An Maida Su Bayi, Ana Bin Wanda Bai Ji Ba Bai Gani Ba, Ana Bigewa’: – Alhaji Turji, Wakilin ’Yan Kwamandojin Dajin Pakai

“Da ya karbi abin magana Alhaji Turji wanda shi ne ya yi magana a madadin kwamandojin da su ka zo sauraren Malam, ya yi maraba da zuwan malam tare da yi masa fatan alkairi da kuma amincewa da su ka yi da su gana da shi da tagwar shi, kasancewar babu wani alkawari da aka yi musu a baya aka cika musu.

“Amma da aka fada masa cewa malamai ne za su zo su same su, sai ya ce bari su saurare su su ji abin da za su zo da shi.

“Ya yi korafi sosai game da yadda aka mayar da Fulani saniyar-ware da yadda aka talauta su da yadda aka mayar da su bayi da buge su a kan hanya da rashin yarda da ko da mashin ne aka ga Bafillatani da shi, sai ce ‘kidnapper’ ne shi.

“Ya fada wa Malam cewar idan ba ta maganar sulhu ba, babu yadda za a yi a kawo karshen wannan abu da ya ke faruwa.

‘Mu Na Da Makaman Da Za Mu Iya Hargitsa Jihar Zamara Gaba Dayan Ta, Amma Mun Yarda A Yi Sulhu’ –Kwamanda Turji

“Ya fada cewar Allah kadai ya san adadin makamai da su ke da su da kuma abin da za su iya yi idan su na son hargitsa jihar gaba dayan ta.

“Ya fada wa malam cewar kashe-kashen kwamandojin da ake yi babu wani abu da ya ke haifarwa sai ma kara samun sabbin dabar ’yan bindiga.

“Ya ce domin su kan su yaran Buharin Daji ne, kuma ya na tabbatar wa da Malam cewar shi ne ya datse wadannan bataliyar. Amma da za a kashe shi, za a samu sama da karin daba talatin.

“A na sa jawabin, Sheikh Sanusi Kutama wanda shi ne wakilin Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya yi kira ga dukkan kwamandojin da cewar don Allah su karbi sulhu ya kuma ba su tabbacin cewar wannan kashe -kashen ba zai haifar da da mai ido ba.

“A jawabin sa Sheikh Gumi ya yi musu nasiha ne da cewar su kasance a matsayin kalifofin Allah nagari a bayan kasa. Kada su kashe wani, kada su yi zina da shaye-shaye da kuma jawo hankalin su game da lafin zubar da jini.

“Ya kuma roke su don Allah su bayar da hadin kai da kuma yarda da cewar za su bari a fara zuwa ana shigo daji ana karantar da su hanyoyin ibadar Allah da kuma koya musu addini.

“A karshe Malam ya raba masu littattafai da kuma atamfofi da yaduka domin kaiwa matan su da su kan su.

“Bayan rufe taro da addu’a, kwamandojin ’yan bindiga sun yi mana rakiya har bakin rafi, daga bisani mu ka karasa Karamar Hukumar Shinkafi, inda mu ka ci abinci da hutawa, sannan misalin karfe 9:16 na dare muka kamo hanyar Gusau inda muka isa karfe 11:30 na dare.

Jerin Sunayen ’Yan Tawagar Sheikh Gumi:

Dakta Muhammad Sulaiman, Limamin Sultan Bello.

Sheikh Sanusi Kutama,

Farfesa Usman Yusuf,

Tukur Mamu, Shugaban Jaridar Desert Herald,

Alhaji Shehu Buba (Tsohon Shugaban Karamar Hukumar Toro, Bauchi),

Wakilan Sarkin Shinkafi,

Malam Sulaiman Abubakar Mahmud Gumi (Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Gumi).

Alhaji Rufa’i Chanchangi

(Tsohon dan Majalisar Tarayya Kaduna).

Manyan Malamai da Alarammomi.

DPO na Karamar Hukumar Shinkafi.

Shugaban Karamar Hukumar Shinkafi.

Alhaji Moyi, matashin da ya yi mana jagora ya kai mu wurin ’yan bindiga.

Share.

game da Author