Matsalar karancin waken soya, wanda a baya Najeriya ce kasar da ta fi sauran kasashe noma shi, a yanzu ya kawo tsaiko da babbar matsala a harkokin kiwon kaji a kasar nan cikin shekarar da ta gabata. Lamarin ya haifar da tsadar kaji da kuma hauhawar farashin waken soya din.
A cikin shekarar da ta gabata dai farashin waken soya ya nunka, kamar yadda wani bincike da PREMIUM TIMES ta gudanar ya tabbatar.
Binciken wanda PREMIUM TIMES ta gudanar, ya nuna cewa buhun waken soya mai nauyin kilogiram 100, wanda ake sayarwa naira 12,000 zuwa naira 13,000, ya rubanya zuwa naira 24,000.
Shugabar Katafariyar Gonar VD&S Farms Folake Aina wadda ke harkar kayan abincin kaji, ta bayyana gagarimar matsalar da masu harkokin kayan abincin kaji su ke fuskanta.
Ta yi bayanin a cikin wata tattaunawar da ta yi da PREMIUM TIMES.
Ta bayyana cewa: “Samun waken soya a yanzu ba karamar matsala ba ce. Idan ka ji ka saya da tsada a yau, to gobe ka koma za ka ji farashin ya tashi. Ka san kuma waken soya shi ne kashi 75 bisa 100 shi ake sarrafawa a yi abincin kaji. Sai kuma masara ta biyo baya.
A makon da ya gabata naira 245 ake sayar da kilogiram daya ciki har da kudin dauko kaya. A jiya kuma farashin ya karu zuwa 290.
“Kuma shi waken soja ya na da karin sinadaran gina jiki, idan babu shi, to kaji ba za su samu isassshen abinci mai jina masu jiki ba. kuma ka san magana ce ake yi ta samar da nama da kwai mai inganci.”
Babban Daraktan Kungiyar Masu Kiwon Kaji ta Najeriya, ‘Poultry Association of Nigeria’ Onallo Akpa, ya bayyana damuwar sa dangane da matsalar tsadar waken soya.
Ya bayyana cewa tan daya na waken soya wanda ake sayarwa naira 160,000 a cikin watan Oktoba, a yanzu ya kai naira 300,000 a cikin wannan wata.
‘Masu Kiwon Kaji Su Na Ta Rufe Gidajen Kiwon Su’
“Yawancin masu gidajen kaji sai rufewa su ke yi, saboda matsalar kayan abinci. Saboda yawancin masu kiwon kajin ko abincin kajin ma ba su iya saye.”
Wannan matsala ta na ci wa harkar kiwon kaji tuwo a kwarya sosai, saboda waken soya sa masara su ne kashi 80 bisa 100 na nau’o’in abincin kaji masu gina jiki.” Haka Akpan ya bayyana.
Shi kuwa Olaseni Olasupo na Profundis farms, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa karancin kayan abincin ta kai masana’antun da ke samar masu da kayan abincin su na maido masu da kudaden su.
“Rashin waken soya zai haifar da karancin sinadaran gina jiki a jikin kaji. Hakan kuwa ya na sa ba a samu kosassun kajin da za su samar da kwayaye da yawa. Idan babu kwayaye da yawa kuwa, to kiwon kaji asara ce babu riba.”
“Ina Mafita?:
Shugaban Kungiyar Manoma Waken Soya na Kasa, Nafiu Abdu, ya kawo shawarar cewa ya zama dole gwamnatin tarayya ta taimaka wa manoma da sauri domin samar da abincin kaji musamman waken soya, ba sai an bari sai cikin watan Yuli ko Agusta ba, sannan wuri ya kure, an makara.”