TARON DANGI : Kungiyoyin kare dimokradiyya sun nemi Buhari ya sauka, ko su tilasta tsige shi

0

Gamayyar kungiyoyin rajin kare dimokradiyya da hakkin jama’a tare da Ofishin Lauya Femi Falana, sun yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya sauka haka nan, ko kuma su tilasta Majalisar Kasa ta tsige shi.

Sun ce ya zama wajibi Buhari ya sauka, idan bay a iya magance matsalar tsaron da ta mamaye gaba dayan kasar nan.

Wannan bukata ta sun a daya daga cikin bukatu biyar da gamayyar kungiyoyin su ka nema a ranar Lahadi, tunda Buhari ya kasa gudanar da babban nauyin da ya rataya kuma ya wajaba a kan sa, a matsayin san a wanda ya wajaba ya wanzar da tsaron al’umma da kuma samar masu walwala da jin dadin dukkan ‘yan Najeriya.

“Shugaba Buhari da gwamnatin sa sun kasa samar da babban nauyin da dokar kasata ta Sashe na 14 2(b) na 1999 ya wajibta a kan su.

Sun kuma yi kakkausan kira ga Buhari ya tsayar da gaggaza wa jama’a da jami’an tsaro ke yi, a daina yin amfani da karfin mulki ana take doka, sannan kuma ya daina nuna fifikon bangaranci, shiyyanci da kabilanci wajen nade-naden mukaman gwamnati da ya ke yi.

Sun kara yin nuni da cewa bangarancin da ya ke nunawa ya na kara ruruta wutar fitinar bangaranci da rikicin kabilanci.

Sannan kuma sun kira ga Buhari ya hana musgunawa, cusgunawa da kuntata wa kafafen yada labarai, t hanyar kakaba masu takunkumin hana su ‘yancin magana da gwamnatin sa keyi.

“Amma idan Shugaba Buhari ya kasa magance wadannan matsaloli, musamman rashin tsaro, to za mu tilasta Majalisar Kasa tacfara shirin tsige shi a bisa yada Sashe na 143 na Kuncin Tsarin Mulkin Najeriya ya tanadar.”

Wasu daga cikin Gamayyar Kungiyoyin Najeriya da su ka sa hannu kan wasikar, sun hada da: Centre for Democracy and Development (CDD), Civil Society Legislative Advocacy Centre (CISLAC), Media Rights Agenda (MRA), Centre for Information Technology and Development (CITAD), Socio-Economic Right and Accountability Project (SERAP), Zero-Corruption Coalition (ZCC), da kuma African Centre for Media and Information Literacy (AFRICMIL).

Sannan akwai kuma: BudgiT Foundation, State of the Union (SOTU), Action International Nigeria, Femi Falana Chamber, HEDA Resource Centre, Open Bar Initiative, Resource Centre, Borno Coalition for Democracy and Progress (BOCODEP), Global Rights, Youth Initiative for Advocacy, Growth & Advancement (YIAGA), Tax Justice and Governance Platform, Women In Nigeria, African Centre for Leadership, da Strategy & Development (Centre LSD).

Share.

game da Author