TALLAFIN 20,000: Maimakon Talakawa, mata da ƴaƴan masu kuɗi ne ma’aikatar jinkai ke rabawa tallafi a Kaduna – Talakawa

0

Wasu mata a jihar Kaduna sun koka kan yadda ake nuna tsangwararan son kai da tafka cuwa-cuwa a wajen rabon kudin tallafi ga mata.

Matan sun ce ma’aikata na karbar cin hanci daga hannun wadanda suka amfana da wannan shiri bayan kuma ma da dama sai an karbi cin hanci daga hannun su ko kuma an nuna fifiko da son kai.

” Ainihin waɗanda aka kirkiro shirin domin su ba su bane ke amfana, abin yakon na ƴan uwa da abokan arziki.

Wata mata ta shaida wa Kamfanin dillancin labaran Najeriya cewa maimakon a rika rabawa talakawa dake cikin ƙungurmin talauci, an koma sai aljihun masu hali da manyan mutane kuɗin ke shiga.

Wata kuma mata mai suna Rabi a Kaduna ta ce kiri-kiri suna zaune za su ga wani ya fito ya kira sunaye sai su shiga a cake musu kudin su su kara gaba. Wasu kana gani za su zo a manyan motoci, wasu ma direbobi ne za su kawo su a shiga da su a danka musu kudin, talakawa kuma da aka yi don su na zaune suna kallo babu yadda suka iya.

Wata mai suna Adama Salisu ta ce bata samu matsala ba wajen karbar kudin, nan da nan a samka mata nata rabon. Sai dai ta ce ita ƴar uwar wata minista ce shine ya sa ta wuce sumul babu matsatsi.

Haka wasu mata suma, sun shaida wa manema labarai cewa sun san wasu da ga cikin jami’an dake raba kuɗin shi ne yasa suka samu nasu rabon babu matsala.

Share.

game da Author