Tsohon ministan sufurin jiragen saman Najeriya, Femi Fani-Kayode ya bayyana ziyarar da tsohon shugaban majalisar Dattawa Bukola Saraki yayi wa tsohon shugaban Kasa a matsayin ihu bayan hari.
Fani-Kayode ya ce bai ga amfanin wannan ziyara ba saboda da shi Saraki a ka hada hannu aka yi tadiye wa Jonathan kafa a 2015.
” Mutumin da dashi aka tadiye wa Jonathan Kafa a 2015, sai kuma yanzu ya zo yace wai ya kawo wa Jonathan Ziyara don a gyara PDP.
Ziyara Saraki ga Jonathan
Shugabannin Jam’iyyar PDP sun kai wa Jonathan ziyarar gaggawa, a daidai lokacin da ake ta watsa ji-ta-ji-ta cewa APC na zarawcin tsohon shugaban kasar domin ya tsaya mata takara a zaben 2023.
Shugaban Kwamitin Sasanta Sabani da Rikicin Mambobin PDP, Sanata Bukola Saraki ne ya shugabanci tawagar da ta kai ziyarar a gidan Jonathan na Abuja.
Daga wadanda su ka kai ziyarar akwai Anyim Pius Anyim, Ibrahim Shema, Liyel Imoke da Ibrahim Dankwambo. A wurin akwai Mulikat Adeola-Akande.
Kwamitin dai ya isa gidan Jonathan a ranar Talata da karfe 1:30n na rana.
Baya ga zawarcin da ake yi wa Jonathan ya koma APC, maganganun da ake yadawa na nuni da cewa za a bashi takarar shugabanci a zaben 2023.
Hakan na faruwa ne a lokacin da wasu gaggan PDP su ka canja jam’iyya zuwa APC.
Sannan kuma ana rade-radin baiwa Sanata Danjuma Goje shugabancin jam’iyyar APC. Goje dai tsohon Sanata ne da a yanzu ba ya kan mukamin sanata.
Saraki ya shaida wa manema labarai bayan ziyarar da su ka kai wa Jonathan cewa Jonathan na nan a jam’iyyar PDP, ba zai koma APC ba.
Ya kara da cewa sun kai masa ziyara ne domin sanar da shi irin kokarin da kwamitin su ya yi wajen sanata rashin jituwa da rikicen jam’iyyar da ya faru bayan zaben 2019.